Home Back

Gwamnatin Tinubu Ta Dawo Biyan Tallafin Man Fetur, An Bayyana Kudin da Take Kashewa

legit.ng 2024/5/18
  • An yi iƙirarin cewa gwamnatin tarayya ta dawo ta ci gaba da biyan tallafin man fetur a Najeriya domin farashin ya yi sauƙi
  • Shugaban kamfanin Rainoil, Gabriel Ogbechie, shi ne ya yi wannan iƙirarin inda ya ce ana kashe kusan N600bn duk wata kan tallafin
  • Ya yi nuni da cewa gwamnati na biyan kusan N400 zuwa N500 kan kowace lita ɗaya ta man fetur da ake amfani da ita

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban kamfanin Rainoil, Gabriel Ogbechie, ya yi iƙirarin cewa gwamnatin tarayya ta dawo biyan tallafin man fetur.

n Ya bayyana cewa gwamnatin ta dawo biyan tallafin ne biyo bayan faɗuwar darajar Naira, cewar rahoton jaridar Nairametrics.

Gwamnatin Tinubu na biyan tallafin man fetur
Gwamnatin Tinubu ta ci gaba da biyan tallafin man fetur Hoto: @DOlusegun Asali: Facebook

Ogbechie ya bayyana hakan ne a yayin wajen wani taro da Stanbic IBTC ya shirya a Legas, rahoton jaridar Businessday ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi nuni da cewa yadda farashin Dala yake N1300 da yawan lita 40m da ake amfani da ita kowace rana a Najeriya, tallafin man fetur ɗin yana kai N400 zuwa N500 kan kowace lita, inda yake lashe aƙalla N600bn a kowane wata.

"Lokacin da shugaban ƙasa ya hau mulki a watan Mayu, ɗaya daga cikin abubuwan da ya ce shi ne an cire tallafi. Eh tabbas tallafi ya tafi saboda nan da nan farashin man fetur ya tashi daga N200 zuwa N500. A wannan lokacin tabbas an cire tallafi."
"A wannan lokacin ana canja Dala kan N460, amma bayan wasu ƴan makonni ta koma N750. A wannan lokacin tallafin man fetur ya fara dawowa."
"Amma yanzu tallafi ya dawo. Idan kuna son sanin yadda farashin man fetur ya kamata ya kasance, ku duba farashin man dizal. Ana sayar da dizal kusan N1300 sannan har yanzu ana sayar da fetur N600."
"Ina gaya muku kyauta cewa a yau akwai tallafin aƙalla N400 ko N500 kan kowace lita. Idan muna shan lita 40m kuma ana biyan N500 kan lita, kusan N20bn ne a rana, N600bn a wata sannan N7.2tr a shekara. Tabbas an dawo da tallafi"

- Gabriel Ogbechie

Asali: Legit.ng

People are also reading