Gwamnatin Tinubu Na Bayar da Tallafin N250,000 Ga 'Yan Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wani shafin Facebook mai suna 'Jobs and Travels' ya sanya wani rubutu inda ya bayyana cewa akwai tallafin N250,000 da gwamnatin APC ta ƙaddamar ga ɗaukacin ƴan Najeriya.
Rubutun wanda aka wallafa a ranar 5 ga watan Mayun 2024, ya samu sama da martani 8,700, sharhi 2,000, da alamar so fiye da 100 ya zuwa ranar Alhamis, 30 ga watan Mayun 2024.
Yawancin masu sharhi kan rubutun sun nuna sun ji daɗin hakan, wanda hakan ya sa wani dandalin duba gaskiya, Dubawa, ya binciki iƙirarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dandalin ya ce ya bi adireshin yanar gizon da aka sanya a cikin rubutun kuma bai samu wani abu ciki da ya nuna a yi rajista ko cancantar samun tallafin gwamnatin tarayya ba.
Maimakon haka, shafin yanar gizon na TGuideWeb ya nuna yadda ƴan Najeriya za su iya samu a ɗauki nauyin bizarsu zuwa ƙasar Amurka.
Dandalin binciken ya kammala da cewa:
"Adireshin yanar gizon da aka sanya a cikin rubutun bai nuna wani shirin tallafi mallakin gwamnatin tarayya ba."
"Bugu da ƙari masu zamba suna amfani da bayanan da ke cikin irin waɗannan shafukan yanar gizon wajen yin munanan ayyuka.
"Saboda haka ya kamata mutane su yi hattara da shafin yanar gizon na bogi."
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashon jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta dawo da shirin bayar da tallafi ga ƴan Najeriya.
Shirin bayar da tallafin kuɗin zai amfani mutane miliyan 75 a cikin gidaje miliyan 50 domin rage musu raɗaɗin talauci da suke fama da shi.
Asali: Legit.ng