Home Back

Harin Sojoji A Kauyen Sudan Ya Kashe Mutum 28

leadership.ng 2024/5/18
Harin Sojoji A Kauyen Sudan Ya Kashe Mutum 28
Sudanese armed forces mark Army Day in Sudan's eastern Gadaref State near the border with Ethiopia on August 14, 2024. Fighting since April 15 between the forces of rival Sudanese generals vying for power has killed at least 3,900 people, according to conservative estimates by the Armed Conflict Location & Event Data Project. (Photo by AFP)

Dakarun sojin Sudan sun kashe akalla mutum 28 a wani hari da suka kai a wani kauye da ke Kudu da Babban Birnin Kasar Khartoum, kamar yadda kwamitin likitocin kasar ya sanar a jiya.

Kungiyar likitocin kasar Sudan ta sanar da cewa, dakarun Kai Dauki Na Musamman (RSF) sun aikata kisan kiyashi a “kauyen Um Adam” mai tazarar kilomita 150 daga Kudancin Birnin a ranar Asabar.

Yakin Sudan tsakanin sojoji a karkashin babban hafsan soji Abdel Fattah al-Burhan, da RSF, karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, ya fara ne a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata.

An kashe dubban mutane da dama, ciki har da mutum 15,000 a wani gari guda a yankin Darfur da yaki ya daidaita, a cewar kwararru daga Majalisar Dinkin Duniya.

Yakin ya kuma raba mutane sama da miliyan 8.5 da muhallansu, tare da lalata ababen more rayuwa da Sudan ta Kudu ke fama da su, ya kuma jefa kasar cikin mawuyacin hali na yunwa.

Harin na ranar Asabar “ya yi sanadin kashe a kalla mazauna kauyuka 28 da ba su ji ba ba su gani ba, sannan fiye da mutane 240 suka jikkata”, in ji kwamitin.

Ya kara da cewa “akwai adadin wadanda suka mutu da kuma jikkatattu a kauyen wadanda ba mu iya kididdige su ba” saboda fadan da ake fama da shi da kuma wahalar isa wuraren kiwon lafiya.”

Kwamitin masu fafutuka na yankin ya bayar da adadin mutane 25 a safiyar yau.

Wata majiyar lafiya a asibitin Manakil da ke da nisan kilomita 80 ta tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa “sun karbi masu raunuka 200, wasu daga cikinsu sun isa a makare”.

Ya kara da cewa “Muna fuskantar karancin jini kuma ba mu da isassun jami’an lafiya.”

Sama da kashi 70 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya na Sudan ba sa aiki a cewar Majalisar Dinkin Duniya, yayin da wadanda suka saura ke karbar mutane da dama fiye da karfinsu kuma suna da karancin kayan aiki.

Ana zargin bangarorin biyu da ke rikici da aikata laifukan yaki da suka hada da kai wa fararen hula hari, da yin luguden wuta ba gaira ba dalili a wuraren da jama’a ke zaune da kuma kwace da hana kayan agaji.

Tun bayan karbe ikon jihar Al-Jazira da ke Kudu da Birnin Khartoum a watan Disamba, RSF ta yi kawanya tare da kai hari ga daukacin kauyuka kamar Um Adam.

Ya zuwa watan Maris, an cinna wuta ga akalla kauyuka 108 da matsugunai a fadin kasar, abin da Cibiyar Resilience da ke Burtaniya ta gano kenan.

People are also reading