Niger: An Shiga Dimuwa Bayan ’Yan Bindiga Sun Shammaci Sojoji, Sun Raunata Wasu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Niger - Akalla sojoji biyu ne suka samu munanan raunuka bayan 'yan bindiga sun farmaki dakarun a jihar Niger.
Maharan sun shammaci sojojin ne a sansaninsu a karamar hukumar Rafi da ke jihar a jiya Litinin 10 ga watan Yuni.
Daily Trust ta tattaro cewa maharan suna kokarin wucewa karamar hukumar Wushishi ne zuwa Mashegu lokacin da suka kai harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban karamar hukumar Rafi, Alhaji Ayuba Usman Katako ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya nuna damuwa sosai.
Katako ya ce sojojin suna ci gaba da karbar kulawa kuma suna samun sauki a asibitin kwararru na IBB da ke birnin Minna., cewar Punch.
Ya bukaci addu'o'i da kuma goyon baya daga jama'a domin ba jami'an tsaro damar dakile matsalar hare-haren 'yan bindiga.
A wani labarin, kun ji cewa Aƙalla mutum 7 ne ƴan bindiga suka kashe a wani sabon harin ta'addanci da suka kai a jihar Neja.
Miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne a wasu ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar.
Maharan da ake zargin ƴan ta’adda ne sun fille kawunan biyu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Kabiru Salihu da Abubakar Karaga.
Asali: Legit.ng