Home Back

Euro 2024: Sifaniya da Italiya - za ku iya tuna hamayya da ke tsakaninsu?

bbc.com 2024/8/21
Spain vs Italy

Asalin hoton, Getty Images

Sifaniya da Italiya za su kece raini a wasa na biyu a rukuni na biyu a ranar Alhamis gasar cin kofin nahiyar Turai, Euro 2024.

Ranar Asabar 15 ga watan Yuni rukuni na biyu ya fara wasan farko, inda Sifaniya ta doke Croatia 3-0, ita kuwa Italiya ta yi nasara a kan Albania 2-1.

Sifaniya ta ci kwallayenta ta hannun Alvaro Morata da Fabian Ruiz da kuma Daniel Carvajal

Albania ce ta fara zura kwallo a ragar Italiya a minti daya da take leda ta hannun Nedim Bajrami daga baya ta farke ta wajen Alessandro Bastoni, sannan Nicolo Barella ya kara na biyu.

Italiya wadda ta lashe Euro 2020 tana da kofin nahiyar Turai biyu, ita kuwa Sifaniya ta dauki uku tun daga 1964 da 2008 da kuma 2012.

Koda yaushe wasan hamayya ake buga wa tsakanin Sifaniya da Italiya, wadanda ke baje kolin fitattun 'yan wasa a duniya.

BBC ta tsakuro muku wasu daga manyan gasa shida baya da aka fafata tsakanin tawagogin.

Nations League karawar daf da karshe - Spain 2-1 Italy (Yunin 2023)

A wasan baya bayan nan da suka kara shi ne wanda Sifaniya ta ci kwallo ta hannun Yeremy Pino da kuma Jesolu, daga baya Italiya ta farke ta hannun Ciro Immobile a bugun fenariti.

Daga nan Sifaniya ta kai karawar karshe ta kuma doke Croatia ta lashe kofin.

Nations League daf da karshe - Spain 2-1 Italy (Oktoban 2021)

Spain vs Italy

Asalin hoton, Getty Images

Karawar da aka yi a San Siro, Sifaniya ta samu kai wa zagayen karshe, bayan da ta ci kwallo biyu ta hannun Ferran Torres tu kan hutu.

An bai wa dan wasan Italiya, Leonardo Bonucci jan kati daga baya Lorenzo Pellegrini ya zare kwallo daya.

A fafatawar Sifaniya ta mamaye wasan da kaso 75 cikin 100 da raba kwallo sau 816 idan ka kwatanta da na Italiya karo 276.

Euro 2020 daf da karshe - Italy 1-1 Spain, 4-2 a fenariti (Yulin 2021)

Spain vs Italy

Asalin hoton, Getty Images

Wani tauraro a Euro 2020 daga Italiya, Federico Chiesa ya fara zura kwallo a ragar Sifaniya a Wembley.

Alvaro Morata, wanda ya shiga wasan daga baya ya farke da ta kai ga bugun daga kai sai mai tsaron raga.

To sai dai kuma shi ne ya buga fenaritin da golan Italiya, Gianluigi Donnarumma ya tare ta kai ga kasar zuwa wasan karshe.

Daga nan Italiya ta doke mai masaukin baki Ingila a Wembley a bugun fenariti.

Euro 2016 - Italy 2-0 Spain (Junin 2016)

Spain vs Italy

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar da Antonio Conte ke jan ragama ta je Stade de France, bayan rashin nasara a hannun Sifaniya a gasar Euro biyu baya.

A wasan ne Giorgio Chiellini da Graziano Pelle suka ci kwallo biyun da ya kai Italiya zagayen daf da na kusa da na karshe, sannan aka kawo karshen shekara takwas da Sifaniya ta yi da kofin Euro.

To sai dai Italiya ta yi rashin nasara a bugun daga kai sai mai tsaron raga a hannun Jamus a zagayen kwata fainals

Euro 2012 wasan karshe - Spain 4-0 Italy (Yulin 2012)

Spain vs Italy

Asalin hoton, Getty Images

Sifaniya lokacin da take rike da kofin duniya da na nahiyar Turai a Euro 2012 - Italiya ta daura damarar ganin ta yi fancale a fafatawar.

To sai dai minti hudu kacal da fara wasa David Silva ya fara cin kwallo a birnin Kyiv daga baya Jordi Alba ya kara na biyu.

Daga baya Juan Mata da kuma Fernando Torres suka ci sauran kwallayen da ta kai Sifaniya ta lashe kofin da tarihin zura kwallaye da yawa a raga a wasan karshen.

Euro 2008 - Spain 0-0 Italy, 4-2 a fenariti (Yunin 2008)

Sifaniya ta je buga wasan a matakin ba ta taba cin Italiya ba a babbar gasar tamaula a karawar da aka tsara yi a birnin Vienna.

Wasan ya yi zafi an kuma gara kwallo, inda Sifaniya ta taka rawar gani koda yake Xavi da Iniesta da Pirlo kowanne ya barar da damarmaki masu kyau.

A karawar ce kociyan Sifaniya, Luis Aragones ya kawo karshen shekara 74 da kasa doke Italiya.

Sifaniya ta kai zagayen daf da karshe a bugun fenariti da cin 4-2, inda Casillas ya tare kwallon Daniele de Rossi da na Antonio di Natale.

Daga baya Cesc Fabregas ya zura na hudu a raga da ta kai Sifaniya zagayen daf da karshe.

Wasannin da za a buga ranar Alhamis 20 ga watan Yuni

1. Karawara rukuni na uku

Filin wasa na Allianz Arena

2. Karawar rukuni na uku

Filin wasa na Deutsche Bank Park

3. Karawar rukuni na biyu

Filin wasa na Veltins Arena.

People are also reading