Home Back

Chelsea ta ɗauki Kellyman daga Aston Villa

bbc.com 2024/7/8
Omari Kellyman

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta kammala ɗaukar ɗan ƙwallon Aston Villa, Omari Kellyman kan £19m.

Mai shekara 18, wanda ya buga wasa shida a kungiyar da ke Villa Park, ya amince da ƙunshin ƙwantiragin kaka shida a Stamford Bridge da cewar za a iya tsawaita shekara ɗaya idan ya taka rawar gani.

Kellyman, ya buga wasa biyu a tawagar Ingila ta matasa ƴan kasa da shekara 20, wanda ya koma Villa a 2022, bayan shekara 10 a Derby County.

Matashin shi ne na biyu da aka kulla cinikayya tsakanin Chelsea da Aston Villa a bana, bayan da Ian Maatsen ya koma Villa Park daga Stamford Bridge.

Haka kuma ɗan wasan Morocco, Hakim Ziyech ya koma Galatasaray daga Chelsea, bayan da ya buga wasannin aro a ƙungiyar Turkiya.

People are also reading