Home Back

Jihar Kebbi Ta Yi Babbar Nasara A Aikin Hajjin Bana – Alhaji Faruk Yaro

leadership.ng 2024/7/1
Jihar Kebbi Ta Yi Babbar Nasara A Aikin Hajjin Bana – Alhaji Faruk Yaro

A yayin da aka kammala aikin hajjin bana a wannan makon, Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruk Yara, Jagaban Gwandu ya bayyana cewa, goyon baya da tallafin da suka samu daga gwamnan jihar, Dakta Nasiru ne ya taimaka musu samun nasarar da suke alfahari da ita.

Faruk ya kuma ce gwamnan ya taimaka musu wajen rashin fuskantar manyan matsaloli tun daga gida Nijeriya har zuwa kasa mai tsarki, gashi kuma cikin ikon Allah an kammala aikin hajji cikin nasara.

Alhaji Faruk ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a garin Makkah ranar Laraba. Ya ce, tun da farko sai da Gwamnan ya cika wa kowanne Alhajin jihar Naira Miliyan 1 na kudin ka’ida na aikin hajji lokacin da dala ta yi tashin gwauron zabi, naira kuma ta fadi warwas.

“Gwamnan ya umarci a dinka wa Hajiyoyinmu yunifam kala biyu su kuma maza aka inganta nasu domin su ji dadin zirga-zirga, wani abin shawa’awa kuma shi ne hatta gwamnan shi ma da yunifam din ya shiga kasa mai tsarki da shi kuma ya yi zirga-zirga cikin garin Makkah.

Haka kuma ba mu fuskanci matsala ba a wajen ciyarwa kamar yadda wasu jihohi suka fuskanta, saboda gwamnanmu ya ba mu izinin samar wa da Alhazanmu karin tsarin samar da ingantaccen abinci duk kuwa da wanda NAHCON ta samar a mastayin shirin kota-kwana. Haka kuma a bangaren hadaya, gwamnan ya biya wa dukkan alhazan Kebbi kudin dabbobin da suka yi hadaya da su, wannan kuma wata hadaka ce na kananan hukumomin jihar da iyalan gwamnan.

Faruq ya bayyana cewa, a halin yanzu suna nazarin tsare-tsare da hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta fito da shi inda daga nan ne za su fito da nasu tsarin tare da inganta shi domin samun cikakkiyar nasara a dawainiyar aikin hajjin shekara mai zuwa.

People are also reading