Home Back

Zargin Tube Sarkin Musulmi: Kallo Ya Koma Sakkwato

leadership.ng 2024/7/6
Zargin Tube Sarkin Musulmi: Kallo Ya Koma Sakkwato

Hankalin al’ummar ciki da wajen kasa ya karkata a Sakkwato, Cibiyar Daular Usmaniyya a bisa ga zargin yunkurin warware rawanin Mai Alfarma Sarkin Musulmi na 20, Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ke jagorantar al’ummar Musulmi a Nijeriya sama da miliyan 85.  

Kungiyoyin addini, shugabanni da sarakuna da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan hadari da illar kokarin cirewa ko barazana ga sarkin wanda ke da girma da daukaka a Yammacin Afirka bisa shaidar da ya samu ta aiwatar da mulkin gaskiya, adalci da wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma tare da jagorantar hadin kai a tsakanin mabambantan addinai.

Yamadidin ya kara ta’azzara ne a bisa ga yadda gwamnatin jihar ta cire rawanin wasu iyayen kasa 15 da Sarkin Musulmi ya nada a jihar tare da canza wa wasu masarautu.

Duka wannan ya biyo bayan rikita- rikitar sarauta a Kano wadda aka canza dokar masarautu tare da cire Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da rusa masarautu biyar da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro tare da mayar da Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

To sai dai tuni gwamnatin Sakkwato ta musanta ko wane irin yunkurin cire rawanin Sarkin Musulmi tana cewar babu kamshin gaskiya ko kadan a ciki.

Yadda Zancen Ya Samo Asali 

Tun farko, hayagagar ta biyo ne bayan da Majalisar Zartaswar Gwamnatin Sakkwato ta aminta da gyaran dokar sarakunan gargajiya tare da aikawa ga majalisar dokoki ta jiha domin amincewa.

Dokar dai za ta rage wa Sarkin Musulmi karfin ikon nada sarakuna ta hanyar bayar da ikon nadawa ga Gwamna kadai wanda wasu suka rika yada cewar dokar ta shafi cire Sarkin Musulmi.

A cewar Kwamishinan Shari’a, Nasir Binji, a dokar, majalisar Sarki za ta ci gaba da rike ikon bayar da wadanda za a nada iyayen kasa da hakimai yayin da gwamna ke da ikon nadawa.

Majalisa Ta Yi Wa Kudurin Dokar Rage wa Sarkin Musulmi Karfin iko Karatu Na 1 Da Na 2 

Duk da musantawa da gwamnati ta yi, a ranar talatar da ta gabata, majalisar dokokin Sakkwato ta fara aiwatar da gyaran fuska ga kudurin dokar nada iyayen kasa ta hanyar rage karfin ikon Majalisar Sarkin Musulmi.

Kudurin da za a yi wa gyara a sashe na 76 kashi na biyu an yi masa karatu na daya da na biyu duka a ranar tare da mika shi a gaban kwamitin da ke kula da kananan hukumomi da masarautu tare da bashi kwana 10 domin tatttaunawa da gabatar da rahoto a gaban majalisar.

Idan majalisa ta aminta da gyaran dokar, kuma gwamnati ta sa mata hannu, shikenan Sarkin Musulmi ba ya da ikon nada iyayen kasa da hakimai domin za a soke gyaran da aka yi wa dokar a 2008 wadda ta bai wa Sarkin Musulmi damar nada iyayen kasar. A bisa ga gyaran wajibi ne sai Sarkin Musulmi ya samu amincewar gwamna kafin nadawa kamar yadda dokar take a 2008.

Babu Maganar Cire Sarkin Musulmi – Majalisa

A yayin da manema labarai suka tuntubi Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Honarabul Kabiru Kware wanda shi ne Mukaddashin Shugaban Majalisar ya bayyana cewar babu ko wace irin magana ta cire rawanin Sarkin Musulmi a gaban majalisar.

“A yanzu ne na fara jin wannan zancen, ina son in tabbatar maku cewar babu wannan maganar a gaban majalisar, shaci- fadi ne kawai. Dokar da kawai ke a gabanmu ita ce wadda ta shafi wa’adin Shugabannin Kananan hukumomi. A yanzu babu kowane irin lamari da ya shafi Majalisar Sarkin Musulmi a gaban mu.”

Dokar Za Ta Karfafa Ayyukan Majalisar Sarkii- Jagoran Majalisa

Shi kuwa Jagoran majalisar dokoki ta jiha, Bello Idris na jam’iyyar APC ya bayyana wa manema labarai cewar ko kadan majalisar ba ta samu ko wace irin doka ta cire rawanin Sarkin Musulmi ba.

Ya ce babu dokar a gabansu, sai dai dokar kara karfafa ayyukan majalisar Sarkin Musulmi domin kara gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

“A cire Sarkin Musulmi a bisa ga wane irin laifi? Gwamnatin jiha tana girmamawa da mutunta majalisar Sarkin Musulmi don haka za su ci gaba da kare martaba da kimarta. Ina kuma son jama’a su yi watsi da wannan zancen su kuma kwantar da hankalinsu.”

A nasa bangaren Kwamishinan Yada Labarai na jihar Sakkwato, Sambo Danchadi ya bayyana cewar ba a canza dokar nada iyayen kasa a jihar ba. Ya kuma ce dangantakar gwamnati da majalisa Sarki kyakkyawa ce.

Wajibi Ne Mu Kare Martabar Sarkin Musulmi – Shettima 

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashiim. Shettima ya bayyana Sarkin Musulmi a matsayin uban al’umma wanda ke da da tambarin magance matsalolin da ke kawo tarnakii ga ci gaban Nijeriya don haka ya zama dole su kare martaba tare da daukaka darajar masarautarsa.

Mataimakin Shugaban Kasa ya yi kalaman ne bayan da daraktan kungiyar Kare Hakkin Musulunci ta (MURIC) Farfesa Isak Akintola ya yi zargin gwamnatin Sakkwato na yunkurin tsige Sarkin Musulmi bayan da ta cire sarakunan gargajiya 15 tare da canza wa wasu masarautu a watan Afrilu. Shettima ya bayyana hakan ne a Katsina A wajen taron gwamnomin Arewa- Maso- Yamma kan magance matsalolin tsaro da wanzar da zaman lafiya a ranar Litinin.

Ka Rika Bincike Kafin Magana – Gwamnatin Sakkwato Ga Shettima

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bukaci Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da a kodayaushe ya rika bincike domin tabbatar da sahihancin labari kafin magana kan muhimmin lamarin da ya shafi kasa.

Gwamnatin ta ce ba ta bukatar a sanar da ita kan ta kare martaba da daga darajar Sarkin Musulmi domin hakki ne da ya rataya a wuyanta. Ta ce gwamnati da al’ummar Sakkwato suna mutunta Sarkin Musulmi da majalisarsa kuma za su iya yin duk mai yiyuwa domin kare martabar Cibiyar Daular Usmaniyya.

A martanin da Abubakar Bawa, Kakakin Gwamnan ya fitar ya bayyana cewar “Mun yi tsammanin Mataimakin Shugaban Kasa zai tuntubi Gwamnan kafin yin wannan maganar a bainar jama’a.

A matsayinsa na mutum mafi daraja ta biyu a kasa ya kamata ya zama yana da cikakken bayani kan lamurran kasa kafin magana a kai.”

Gwamnan ya ce a matsayin Shettima na jigo kuma uban al’umma ya dace a ce yana da sahihan bayanai da hujjoji kafin zartas da hukunci kan batutuwan da masu yunkurin hada husuma ke yi da gurbatattun ma’abota amfani da Soshiyal midiya suka yada bisa ga gurbatacciyar manufa.

Ya ce “Gaskiyar zancen shi ne babu ko wane irin yunkurin cire rawanin Sarkin Musulmi kuma ba a taba yi masa ko wace irin barazana ba. Sarkin Musulmi yana samun duk wata dama da iko kuma ba mu taba hana masa ko wane irin ‘yanci ko dama ba.”

Wajibi Ne Gwamnoni Su Mutunta Sarakuna – Atiku Abubakar

Jagoran ‘yan adawa a Nijeriya kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya bi sahun Mataimakin Shugaban Kasa Kashiim Shettima kan wajibcin kariyar mutuncin Cibiyar Daular Usmaniyya da sauran sarakuna.

Wazirin Adamawa ya bukaci da a sanya sarakuna a cikin kundin tsarin mulkiin Nijeriya. Ya ce hakan ne zai kare martabar masarautun daga barazanar rugujewa a bisa ga katsalandan din da gwamnoni ke yi wa sarakunan da ke karkashin su.

Dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP a 2023 wanda ya bayyana hakan a ranar Talata ya ce ya zama wajibi gwamnoni su rika mutunta sarakuna kamar yadda ya zama wajibi a kare martabar masarautun.

Majalisar Sarkin Musulmi Ta Ki Cewa Komai 

Sakataren Majalisar Sarkin Musulmi kuma Danburam Sakkwato, Sa’idu Maccido ya ki aminta ya bayyana wani abu kan zargin. Ya ce wajibi ne ya tuntubi Majalisar Sarkin Musulmi kafin furta ko wane irin abu kan lamarin.

Sai dai wani a Majalisar da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewar ba wannan ne karon farko da aka bukaci gabatar da gyaran fuska ga dokar ba don haka ba bakon abu ba ne.

“An yi gyaran dokar Kananan Hukumomi a lokacin mulkin tsohon Gwamna, Aliyu Wamakko. Hasalima wannan gyaran dokar ne ya bai wa Sarkin Musulmi ikon nada sarakuna ba tare da sanya bakin Gwamna ba. Don haka ban ga wani laifi don a yanzu wata gwamnati ta ga bukatar canza dokar zuwa yadda take a baya ba. Dokar da ake son a yi wa gyara ba ta da ko wace irin alaka da cire rawanin Sarkin Musulmi ko nada shi wanda shi ne abin da mutane da yawa ba su sani ba.”

Ya ce dokar da gwamnatin Sakkwato ta aikawa majalisa ana kiran ta dokar Kananan Hukumomi ta 2008 wadda ta kunshi kawai nadawa ba wai cire iyayen kasa da hakimai ba. Ya ce dokar nada Sarkin Musulmi daban take.

Har ila yau, Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewar akwai kyakkyawar alaka tsakaninta da Majalisar Sarkin Musulmi a karkashin jagorancin Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar. A cewarta babu ko wace irin baraka a tsakaninsu.

A kan wannan, gwamnatin ta bayyana cewar ko kadan babu kamshin gaskiya a ikirarin da kungiyar Kare Hakkin Musulunci (MURIC) ta yi na cewar tana shirin tube rawanin Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

Gwamnatin ta bayyana cewar akwai mamakin yadda kungiyar MURIC da ke ikirarin kare martabar musulunci za ta zubar da kimarta wajen hada hannu da masu kokarin hada husuma da makiya ci gaba wajen kirkirar labarin karya wanda ba ya da tushe domin gurbata kyakkyawan yanayi da sanya fargaba a zukatan al’ummar jihar Sakkwato masu son zaman lafiya da bin doka.

Gwamnan ta bakin Kakakinsa, Abubakar Bawa a martanin da ya fitar ya bayyana cewar suna da tabbacin MURIC ba irin kungiyar da makiya za su yi amfani da ita ba ne a kokarin kawar da hankalin jama’ar Sakkwato da kasa bakidaya kan ayyukan ci gaban da ke gudana a jihar.

“Muna son tabbatarwa MURIC cewar wannan gwamnatin kamar sauran gwamnatocin da suka gabata suna mutuntawa da girmama Majalisar Sarkin Musulmi lokaci mai tsawo tun kafin a kirkiro kungiyar.”

Gwamnatin ta ce Majalisar Sarkin Musulmi wadda ke da dadadden ingantaccen tarihi tana da matukar tasiri ga al’ummar jihar Sakkwato don haka suke ci gaba da rike ta da matukar girma da muhimmanci.

A cewarta wannan ba shine karo na farko da aka kirkiri labari irin wannan domin a nuna akwai tsamin dangantaka tsakanin gwamnatin Sakkwato da Majalisar Sarkin Musulmi ba domin ko a watannin baya an yada labari makamancin wannan wanda suka musanta.

“Ga yadda abubuwa ke tafiya wadannan makiya ci gaba ba su yi kasa a guiwa ba a kokarin da suke yi wanda ba zai yi nasara ba domin gurbata kyakkyawar alakar da ke akwai tsakanin gwamnatin jiha da Majalisar Sarkin Musulmi.”

“Ya dace MURIC ta yi bincike domin gano ko akwai lokacin da gwamnati ta taba yin tuhuma, gargadi ko wata irin barazana ga Sarkin Musulmi. Haka ma muna son kungiyar ta sani bunkasa sha’anin addinin Musulunci da daga darajarsa shi ne ajanda ta biyu cikin ajandodi 9 na gwamnatin Ahmed Aliyu, haka ma jihar Sakkwato wadda ita ce Cibiyar Daular Usmaniyya, kashi 100 na al’ummarta Musulamai ne.”

A cewar gwamnatin a kodayaushe tana tuntubar Mai Alfarma Sarkin Musulmi kan abubuwan da suka shafi jiha haka ma tana girmama shawarwari da gudunmuwar da yake bayarwa wadanda suna amfani da su wajen aiwatar da manufofin gwamnati.

Gwamnatin ta ce a kan cirewa da yi wa Sarakuna 15 canjin masarautu ta dauki matakin ne a bisa ga kama su da laifin rikicin filaye da samun hannunsu ga gurbata sha’anin tsaro da sauransu.

Shawarar Farko Da Shettima Ya Baiwa Gwamnan Kan Sarkin Musulmi A 2023

A gaisuwar Sallah Babba a shekarar da ta gabata da Mataimakin Shugaban Kasa ya kawo wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana wa Gwamna Aliyu karara cewar ka da ya bari a samu sabani tsakaninsa da Sarkin Musulmi.

“Arewa muna cikin matsala, ga rashin zaman lafiya ga talauci, ya dace mu hada kai domin mu tsira. Na kira Gwamna na fada masa duk yadda zai yi ka da ya bari baraka ta shiga tsakaninsa da Sarkin Yamma (Sanata Wamakko).

“Kuma kar ya bari baraka ta shiga tsakaninsa da Sarkin Musulmi, ya girmama shi ya mutunta shi domin babban ginshki ne ba wai a Arewa Maso Yamma kawai ba, har a Afrika ta Yamma da duniyar Musulmi. Babu zaman lafiya idan babu ci gaba haka ma babu ci gaba idan babu zaman lafiya.”

“Abu ne mai sauki a gare shi ya zauna lafiya da Sanata Wamakko a kan ya samu sabani da shi haka ma abu ne mai sauki ya zauna lafiya da Sarkin Musulmi a kan ya raba gari da shi. Abin da hadin kai bai kawo mana ba rashin hadin kai ba zai taba kawo mana shi ba. Sarkin Musulmi shugaban mu ne muna girmama shi muna martaba shi.” Ya bayyana a gaban gwamna da Sanata Wamakko.

Asalin Zargin Baraka

Masu fashin bakin lamurran yau da kullum na ganin kyakkyawar alakar da ke akwai tsakanin Majalisar Sarkin Musulmi da Sanata Aminu Waziri Tambuwal wanda ya shugabanci jihar mulkin wa’adin zango biyu ce asalin zargin barakar da ke akwai tsakanin jigogin jam’iyyar APC a jihar da Majalisar Sarki wadanda ke da tsamin dangantaka da Tambuwal wanda Sarkin Musulmi ya nada Mutawallen Sakkwato.

Jama’a da dama na ganin wannan zargin na adawa tsakanin jagororin siyasar jihar da kusancin daya bangaren da kauracewar daya bangaren ga Majalisar Sarkin Musulmi kusan shi ne ya haddasa yamadidi da zargin da jama’a ke yi.

Idan aka yi waiwayen baya za a ga magoya bayan jam’iyyar APC tun a zaben 2019 sun rika ikirarin canza Sarkin Musulmi idan suka samu nasarar lashe zabe. Hasalima akwai lokacin da wasu matasa a yayin wata zanga- zanga- suka rika jiifar Fadar Sarkin Musulmi tare da ambaton “Sabon Gwamna, Sabon Sarki”.

Wasu da dama na ganin hakan ya sanya fargaba da zullumi ga al”umma wadanda ke ganin idan suka samu nasara za su iya taba martabar gidan Mujaddadi Danfodiyo.

Sai dai a bayyane jama’a sun shaidi rike girma da mutuncin Majalisar Sarki da Mai Alfarma Sarkin Musulmi ke yi a kodayaushe ta hanyar zama uban kowa tare da nesata kansa da majalisarsa ga goyon baya ko shiga lamurran kowace jam’iyya. Hasalima kofarsa ta kasance bude ga mabambantan jam’iyyu da ‘yan takararsu wadanda yake baiwa shawarwarin gudanar da siyasa mai tsafta da aiwatar da yekuwar neman zabe ba tare da tashin- tashina ba.

Haka ma Sarkin Musulmi kan bukaci ‘yan siyasar da ke tururuwar zuwa fadarsa neman sanya albarka da su gudanar da zabe ba tare da zubar da jini ba da aminta da sakamakon zabe da kuma rungumar kaddarar faduwa zabe tare da aiwatar da mulkin gaskiya da adalci da kai kasa da al’ummarta a tudun mun tsira bayan samun nasara.

People are also reading