Home Back

Tsananin zafi na tunkarar Yammacin Afirka- Bincike

rfi.fr 2024/5/2

Hukumar da ke nazarin sauyin yanayi da yadda yake tasiri kan muhallin dan Adam ta kasa da kasa ta bayyana fargaba, game da yadda barazanar tsananin zafi ke tunkarar kasashen da ke yammacin nahiyar Afrika.

Wallafawa ranar: 18/04/2024 - 18:33

Minti 1

Rahoton ya tabbatar da cewa, matsalar dumamar yanayi ce ta haifar da tsananin zafi a wasu yankuna na Afirka.
Rahoton ya tabbatar da cewa, matsalar dumamar yanayi ce ta haifar da tsananin zafi a wasu yankuna na Afirka. © TheGuardian

A wani rahoto da hukumar ta fitar ta kuma ba da shawara ga kasashen da ke yankin Sahel cewa su fitar da shirye-shiryen da suka kamata tare da yin gargadi ga al'ummunsu game da tsananin zafin dake tunkarar su domin daukar matakan kan da garki.

A cewar rahoton tun a karshen watan Maris da kuma farkon watan Afrilu, an shaida yadda aka rinka fuskantar tsananin zafi cikin dare ko da rana sama da 40 na ma'aunin Celsius.

Yanayin matsanancin zafin yafi kamari a kasashen Mali da Burkina Faso, in ji rahoton hukumar.

Domin a cewar rahoton Hukumar ta World Weather Attribution sama da shekaru 200 ba'a fuskanci makamancin wannan yanayi na zafi ba a sassan duniya.

Tsananin zafin ranar da ake samu a banya-bayan nan shi ne ya ja hankalin tawagar masana kimiyyar yanayi na Hukumar ta WWA gudanar da wannan bincike cikin gaggawa.

People are also reading