Home Back

Rushe Masarautu: Matsayar Majalisar Dokokin Jihar Kano kan Maganar Karbar na Goro

legit.ng 2024/7/3
  • Majalisar dokokin Kano ta musanta labarin dake zargin sun karbi na goro daga gwamnatin jiha domin rushe masarautun Kano guda biyar
  • A sakon murya da babban sakataren yada labaran majalisar dokokin jihar, Kamaluddin Sani Shawai ya aikewa manema labarai ya ce labarin karya ne
  • Ya ce 'yan majalisar Kano ba su karbi cin hancin motoci da kudade ba kamar yadda wasu da ya yi zargin makiya Kano ne ke yadawa a kafafen labarai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Majalisar dokokin jihar Kano ta musanta labarin da ke cewa ‘yan majalisa sun karbi cin hanci domin rushe masarautun jihar biyar.

Babban sakataren yada labaran majalisar dokokin jihar kano kuma mai magana da yawun shugaban majalisar dokokin, Kamaluddin Sani Shawai ne ya musanta zargin.

Majalisar Kano
Majalisar Kano ta musanta karbar cin hanci domin rushe masarautu Hoto: Kano State House of Assembly Asali: Facebook

A cikin sakon murya da ya aikewa manema labarai wanda wakiliyar Legit ta saurara, Shawai ya bayyana labarin da kagagge wanda babu gaskiya a cikinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Makiya Kano ke yada labarin karya,’ Shawai

Mai magana da yawun shugaban majalisar dokokin, Kamaluddin Sani Shawai ya zargi masu yada labarin cewa an bawa majalisar cin hanci da makiya Kano ne da basa son zaman lafiya.

Majalisar dai ta rushe masarautun jihar guda biyar, tare da nada sabon sarki kwanaki kadan bayan sun karbi motocin alfarma kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Amma majalisar ta musanta cewa an ba ta motocin ne a matsayin cin hanci domin dabbaka bukatar gwamnatin jihar.

Ya bayyana cewa:

“Wannan labari ne da ba shi da tushe ballantana makama. Yan majalisar jihar Kano ‘yan majalisa ne da al’ummar jihar Kano suka zabe su bisa cancanta da sanin makama, masu ilimi ne da hangen nesa.

Gwamnatin Kano ta sayawa yan majalisa motoci

A baya mun kawo muku labarin cewa gwamnatin jihar Kano karkashin Abba gida-gida ta sayawa 'yan majalisar jihar motocin alfarma 41.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe N2.6bn wajen sayen motocin, inda kowane dan majalisa ya karbi motar alfarma da akalla ta kai N68m.

Asali: Legit.ng

People are also reading