Home Back

Dalilin da ya sa gwamnati ta tsaida shekaru 18 a matsayin mafi karancin shekarun shiga jami’a – Minista

premiumtimesng.com 2024/5/17
Dalilin da ya sa gwamnati ta tsaida shekaru 18 a matsayin mafi karancin shekarun shiga jami’a – Minista

Gwamnatin Najeriya ta sanar cewa daga yanzu shekaru 18 ne mafi karanci shekaru na shiga jami’a daga makarantar sakandare.

Ministan Ilimi Tahir Mamman ne ya sanar da haka yayin da ya je duba jarrabawar (UTME) da ke gudana a Bwari Babban Birnin Tarayya Abuja.

Mamman ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki domin rage yadda iyaye ke tilasta ‘ya’yan su shiga jami’a tun kafin su san ciwon kan su yadda ya kamata.

Ya Kuma ce wannan mataki da suka dauka dai-dai yake da tsarin ilimi na 6-3-3-4.

“Yanzu mafi karancin shekarun shiga jami’a shine 18 amma mun ga dalibai masu shekaru 15, 16 dake karatu a jami’a.

“Muna kira ga iyaye da su rigerigen tura ‘ya’yan su jami’a tun ba su gama sanin meye gaban su ba da bayan su.

“Za mu yi kokarin duba wannan matsala domin yara da dama da suka shiga jami’a da wuri ba su kai matsayin hankalin da za su iya gane halin da ake ciki na rayuwa da karatu ba.

Bayan haka ya ce gwamnati za ta sa a fara horas da daliban firamare da sakandare sana’o’in hannu domin samar musu abin dogaro ko da tun kafin su kammala karatu.

“Kashi 20% ne kadai ke shiga jami’a ko kwalejin kimiya da fasaha inda kamata ya yi sauran kashi 80% da za su rage na da sana’ar hannun da za su iya dogaro da shi.

Shugaban hukumar shirya jarabawar JAMB Fabian Benjamin ya jinjina matakin tsayar da shekaru 18 na shiga jami’a da gwamnati ta yi yana mai cewa hakan ya yi dai-dai da tsarin ilimi na 6-3-3-4.

People are also reading