APC Ta 'Tona Asirin' Ayyukan da Gwamna Fubara Ya Kaddamar a Ribas
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - An samu musayar yawu tsakanin jam'iyyar APC da gwamnatin jihar Ribas kan ayyukan da gwamna Siminalayi Fubara ya kaddamar.
Gwamna Fubara ya kaddamar da ayyukan ne yayin bikin cikar shi shekara daya kan karagar mulki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito APC na cewa ba gwamna Fubara ne ya yi ayyukan ba a lokacin da ya kafa gwamanti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin da ya yi bikin cika shekara daya kan karaga, gwamna Fubara ya kaddamar da ayyuka a jihar Ribas ciki har da manyan tituna.
Cikin titunan da ya kaddamar akwai hanyar Etewo Eleme da hanyar Andoni Ogoni Obobo da hanyar Kalabari a jihar Ribas.
Amma sai dai jam'iyyar APC a jihar ta yi martani inda ta ce ba gwamna Fubara ba ne ya fara ayyukan da kansa, rahoton Tribune.
Ta ce dukkanin ayyukan tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ne ya fara su a lokacin da yake gwamnan jihar.
Sai dai a na shi bangaren, gwamna Siminalayi Fubara ya ce babu kamshin gaskiya a cikin maganar da APC ta yi.
Kwamishinan yada labarai na jihar Ribas, Barista Joseph Johnson ya ce gwamna Fubara ne ya fara ayyukan kuma ya kammala su.
Har ila yau, kwamishinan ya ce akwai sauran ayyukan da gwamna Fubara ya fara amma nan gaba za a karasa su da yardar Allah.
A wani rahoton, kun ji cewa yayin murnar cika shekara daya a kan mulki, gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya bayyana yadda aka bar masa tarin bashi.
Har ila yau, Fubara ya kuma bayyana dalilin da yasa tsohon gwamna Nyesom Wike ya fara yakarsa tun wata uku da zamansa gwamna.
Asali: Legit.ng