Home Back

Binciken Gwamnatin El-Rufai: Ko Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Za Ta Rusa Mai Rusau?

leadership.ng 2024/5/19
Binciken Gwamnatin El-Rufai: Ko Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Za Ta Rusa Mai Rusau?

Kallo ya koma kan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna yayin da ta kafa kwamitin mutum 13 domin gudanar da bincike a kan harkokin kudaden da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasir el-Rufai ta gudanar a tsawon shekara takwas da gwamnatin ta kwashe a kan karagar mulki.

Har ila yau, majalisar ta dora wa kwamitin alhakin binciken kudaden tallafi da na bashin da gwamnatin el-Rufai ta amso.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaura a zauren majalisar dokokin jihar, Hon. Yusuf Mugu ne ya gabatar da kudurin a zauren majalisar a tsakiyar makon nan.

Haka kuma majalisar ta ce za ta bi diddigin kudaden da tsohuwar gwamnatin ta kashe wajen aiwatar da manyan ayyuka a tsawon wa’adin mulkin el-Rufai tun daga 2015 zuwa 2023.

Shugaban majalisar, Hon. Yusuf Dahiru Liman ya nemi ‘yan kwamitin da su gayyaci duk masu ruwa da tsaki da suke da alaka da binciken domin su amsa tambayoyi kan lamarin.

Ya tabbatar da cewa za a gudanar da binciken ne bisa adalci tare da bai wa koya damar gabatar da gaskiyarsa.

Shi dai Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana cewa ya gaji bashin dala miliyan 587 da naira biliyan 85 da kuma kwangiloli har 115 daga gwamnatin el-Rufai.

Ya nuna damuwarsa kan illar da bashin ke janyo wa jihar, wanda ya ce bashin ya hana biyan albashin ma’aikatan jihar.

Sai dai da yawa sun yi watsi da kalaman gwamnan bisa cewa da sa hannunsa aka karbi bashin lokacin da yake kujerar Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya.

Masu sharhin al’amuran yau da kullum na ganin wannan yunkurin na majalisa na da alaka da siyasa bisa yadda ake ganin kamar dangantaka ta dan fara tsami a tsakanin el-Rufai da Gwamnatin Tinubu wacce ta yi masa ta leko ta koma a kan mukamin minista, shi kuma ya fara hada kai da wasu ‘yan adawar jam’iyya mai mulki.

Abin da mutanen Kaduna ke jiran gani shi ne, ko majalisar za ta iya rusa mai rusau kamar yadda el-Rufai ya yi farin jini da sunan a yakin neman zaben 2015, ganin cewa galibin wadanda ya yi aiki da su suna nan birjik a cikin gwamnatin da ke ci wadda take korafi a kan bashin da tsohuwar gwamnatin ta ci?

People are also reading