Masarautun Kano: Kotu Ta Sanya Lokacin Fara Sauraran Shari'ar, Ta Fadi Ka'idar da Za a Bi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Kotu ta sanya ranar fara sauraran shari'ar da aka shigar kan rigimar masarautun jihar Kano.
Kotu ta sanya yau Alhamis 06 ga watan Yuni domin sauraren shari'ar ta manhajar Zoom.
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano karkashin jagorancin Mai shari'a, A.A Liman za ta fara jin bahasin bangarorin biyu, cewar Aminiya.
Idan baku manta ba, kotun ta sanya Litinin 3 ga watan Yuni a matsayin ranar fara sauraran karar wadda aka dage sakamakon yajin aikin kungiyoyin Kwadago.
Daya daga cikin manyan hakimai a fadar Kano, Sarkin Dawaki Babba, Alh. Aminu Babba Dan Agundi wanda kuma Hakimin Nassarawa ne shi ya shigar da karar a gaban kotun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan Agundi yana kalubalantar Majalisar Dokokin jihar da Gwamna Abba Kabir kan rushe masarautun jihar 5 da gwamnatin Ganduje ta kirkiro.
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng