Home Back

Sanusi II vs Aminu Ado: Sarkin Kano Na 15 Ya Rubuta Takarda ga Ƴan Sanda Kan Bikin Sallah

legit.ng 2024/7/7
  • Yayin da ake ci gaba da rigimar sauratar Kano, ta tabbata Sarki na 15, Aminu Ado Bayero zai yi hawa domin bukukuwan sallah
  • Aminu Ado ya rubuta takarda ta musamman ga jami'an 'yan sanda domin samar da tsaro ga al'ummar jihar Kano yayin bukukuwan
  • Wannan na zuwa ne yayin da Aminu Ado ke shirye-shiryen hawa a babbar salla duk da kasancewar Sarki Muhammadu Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya rubuta takarda ta musamman ga kwamishinan ƴan sanda a jihar.

Aminu Ado ya rubuta takardar domin neman gudunmawar tsaro yayin bukukuwan sallah babba da za a yi a jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da sakatare na musamman ga Aminu Ado ya fitar a ranar 10 ga watan Yuni, cewar Daily Trust.

"Ina rubuta wannan takarda a madadin Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero bayan umarnin kotu ta bukaci mayar da shi kan karaga."
"Ina amfani da wannan dama wurin isar da godiyarsa gare ku kan kokarin samar da tsaro da kuka yi musamman lokacin rigimar sarauta, jama'ar Kano suna godiya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mai Martaba, ya roki shirya jami'an tsaro na musamman domin bukukuwa salla daga ranar Lahadi 16 ga watan Yuni zuwa Alhamis 20 ga watan Yuni, za a fara hawa daga fadar Nasarawa."
"Wannan hawa da bukukuwan sallah na da muhimmaci a bangaren addini da kuma aladu da ke jawo hankalin jama'a a ciki da wajen jihar Kano."

- Aminu Ado Bayero

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading