Majalisa Ta Ɗauki Mataki Kan Korar Daraktoci da Manyan Ma'aikata a Bankin CBN
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta ɗaura niyyar gudanar da bincike kan yadɗa aka yi aka raba ƴan Najeriya akalla 60 da aikinsu a babban bankin Najeriya (CBN).
Majalisar ta cimma wannna matsaya bayan amincewa da kudirin hanzari da Honorabul Jonathan Gbefwi (SDP, Nasarawa) ya gabatar a zauren ranar Laraba.
Da yake gabatar da kudirin, ɗan majalisar ya ce ma'aikata sama da 60 sun rasa aikinsu a CBN a wani ɓangare na kokarin sake fasalin ayyukan babban bankin, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce abin da CBN ya aikata ya haifar da damuwa da cece-kuce a tsakanin masu ruwa da tsaki kama daga ma’aikatan da aka kora, kungiyoyin kwadago da sauran jama’a.
Dan majalisar ya koka da cewa wadanda CBN ya kora kwararru ne kuma ƙasahen Turai da Amurka ka iya zuwa su ɗauke su, su bar Najeriya na ci baya.
Gbefwi ya nuna damuwarsa cewa irin waɗannan matakai na kora ba tare da saurare ma'aikatan ko bincike ba ka iya jawo ma ƙasar nan koma bayan da ba a tunani.
Idan baku manta ba a rahoton da muka kawo maku, waɗanda CBN ya kora sun haɗa da daraktoci. mataimakansu, manyan manajoji da ma'aikata.
Da yake jawabi kan aikin daraktoci, Honorabil Gbefwi ya ce:
“Wa’adin darakta bisa ka’idar aikin gwamnati shi ne wa’adi biyu na shekara hudu watau shekaru takwas kenan ko kuma shekarun aiki 60, duk wanda ya fara cika shikenan.
"Wannna ya sa suka zama kamar manyan sakatarori. Abin tambayar shi ne za a iya maye gurbin kwarewar waɗanda aka kora cikin sauƙi?"
Da take amincewa da kudirin, majalisar ta umurci kwamitocin kula da harkokin banki da kuma tsarin tarayya da su duba yadda ake garambawul a CBN.
Kuma ta umarci su bincine dalilin da ya sa akw rage yawan ma'aikata a babban bankin kana su dawo da rahoto cikin makonni huɗu, The Cable ta ruwaito.
A wani rahoton kuma Shugaba Bola Tinubu ya bayyana wadanda suka masa sharar fage har ya samu damar zama zaɓaɓɓen shugaban kasa a Najeriya.
Bola Tinubu ya bayyana haka ne a yau Laraba yayin da yake kaddamar da sabon taken Najeriya a majalisar dattawan kasar.
Asali: Legit.ng