Home Back

Majalisa Ta Ɗauki Mataki Kan Korar Daraktoci da Manyan Ma'aikata a Bankin CBN

legit.ng 2024/7/5
  • Batun korar daraktoci da manyan ma'aikata a babban bankin Najeriya ya ja hankalin majalisar wakilan tarayya ranar Laraba
  • Majalisar za ta binciki yadɗa aka yi aka rubutuwa ma'aikatan takardar kora a CBN bayan ta amince da wani kudiri da aka gabatar
  • Ta bai wa kwamitocin biyu aikin gudanar da wannan bincike kuma su dawo da rahoton abin da suka gano cikin makonni huɗu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta ɗaura niyyar gudanar da bincike kan yadɗa aka yi aka raba ƴan Najeriya akalla 60 da aikinsu a babban bankin Najeriya (CBN).

Majalisar ta cimma wannna matsaya bayan amincewa da kudirin hanzari da Honorabul Jonathan Gbefwi (SDP, Nasarawa) ya gabatar a zauren ranar Laraba.

Majalisar dokoki ta ƙasa.
Majalisar wakilai za ta duba yadda ake sallamar ma'aikata a CBN Hoto: HouseNGR Asali: Facebook

Da yake gabatar da kudirin, ɗan majalisar ya ce ma'aikata sama da 60 sun rasa aikinsu a CBN a wani ɓangare na kokarin sake fasalin ayyukan babban bankin, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce abin da CBN ya aikata ya haifar da damuwa da cece-kuce a tsakanin masu ruwa da tsaki kama daga ma’aikatan da aka kora, kungiyoyin kwadago da sauran jama’a.

Dan majalisar ya koka da cewa wadanda CBN ya kora kwararru ne kuma ƙasahen Turai da Amurka ka iya zuwa su ɗauke su, su bar Najeriya na ci baya.

Gbefwi ya nuna damuwarsa cewa irin waɗannan matakai na kora ba tare da saurare ma'aikatan ko bincike ba ka iya jawo ma ƙasar nan koma bayan da ba a tunani.

Idan baku manta ba a rahoton da muka kawo maku, waɗanda CBN ya kora sun haɗa da daraktoci. mataimakansu, manyan manajoji da ma'aikata.

Da yake jawabi kan aikin daraktoci, Honorabil Gbefwi ya ce:

“Wa’adin darakta bisa ka’idar aikin gwamnati shi ne wa’adi biyu na shekara hudu watau shekaru takwas kenan ko kuma shekarun aiki 60, duk wanda ya fara cika shikenan.
"Wannna ya sa suka zama kamar manyan sakatarori. Abin tambayar shi ne za a iya maye gurbin kwarewar waɗanda aka kora cikin sauƙi?"

Da take amincewa da kudirin, majalisar ta umurci kwamitocin kula da harkokin banki da kuma tsarin tarayya da su duba yadda ake garambawul a CBN.

Kuma ta umarci su bincine dalilin da ya sa akw rage yawan ma'aikata a babban bankin kana su dawo da rahoto cikin makonni huɗu, The Cable ta ruwaito.

Tinubu ya faɗi waɗanda suka taimake shi

A wani rahoton kuma Shugaba Bola Tinubu ya bayyana wadanda suka masa sharar fage har ya samu damar zama zaɓaɓɓen shugaban kasa a Najeriya.

Bola Tinubu ya bayyana haka ne a yau Laraba yayin da yake kaddamar da sabon taken Najeriya a majalisar dattawan kasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading