Home Back

Hauhawar Farashin Siminti: Majalisa Ta Bai Wa Dangote, BUA, Da Sauransu Wa’adin Kwanaki 14 Su Bayyana Gabanta

leadership.ng 2024/5/20
Hauhawar Farashin Siminti: Majalisa Ta Bai Wa Dangote, BUA, Da Sauransu Wa’adin Kwanaki 14 Su Bayyana Gabanta

Majalisar Wakilai ta bayar da wa’adin kwanaki 14 ga kamfanonin simintin Dangote, BUA, Lafarge, Asaka da Eagle da su gurfana a gaban kwamitinta na hadin gwiwa kan hauhawar farashin siminti a fadin Nijeriya ba bisa ka’ida ba.

Shugaban kwamitin majalisar mai kula da ma’adanai, Hon. Gaza Gbefwi, ya bayar da wannan umarnin a yayin zaman kwamitin a ranar Talata a Abuja domin gudanar da bincike kan karin farashin siminti a Nijeriya da kamfanonin siminti suka yi.

Majalisar ta amince da kudiri kan “gurfanar da kamfanonin siminti kan karin farashin siminti ba bisa ka’ida ba a Nijeriya.” In ji shi

Sai dai a zaman da aka yi na binciken wasu kamfanonin siminti, guda biyar daga cikinsu da suka hada da Dangote, BUA, Lafarge, Asaka da Eagle sun ki amsa gayyata kuma ba su tura wani wakili da zai yi wa ‘yan majalisar bayani ba.

Da yake yanke hukunci kan lamarin, Hon. Gbefwi ya yi gargadin cewa, majalisar wakilai ba ta samu wani umarnin kotu da ya hana kamfanonin amsa gayyatar ba, don haka, dole ne wadanda aka gayyata su bayyana a gaban kwamitin majalisar cikin kwanaki 14.

People are also reading