Home Back

Tinubu Ya Amince da Yi Wa Ma'aikata Karin Albashi, Bayanai Sun Fito

legit.ng 2024/5/19

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da yin ƙarin albashi ga ma’aikatanta da kaso 25% zuwa kaso 35%.

Ma’aikatan da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta yi wa ƙarin albashi sun haɗa da masu karɓar albashi na bai-ɗaya na CONPSS, CONRAISS, CONPOSS, CONPASS, CONICCS da CONAFSS.

Tinubu ya yi karin albashi ga ma'aikata
Gwamnatin tarayya ta yi wa ma'aikata karin albashi Hoto: @DOlusegun Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na hukumar kula da albashi ta ƙasa, Emmanuel Njoku, ya fitar.

Ku dakaci ƙarin bayani.....

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

People are also reading