Home Back

Tinubu ya mayar wa Kwankwaso martani

bbc.com 2024/7/7
.

Asalin hoton, Kwankwaso/Twitter

Musayar kalamai sun barke tsakanin fadar shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu, da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP kuma tsohon gwamanan Kano Sanata Rabi'u Musa kwankwaso kan zargin da kwankwason ya yi na cewar gwamantin Bola ahmed Tinubu na ƙokarin ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar ta Kano.

Yayin wani taron ƙaddamar da aiki da gwamnatin jiha Kano ta gudanar, an jiyo Kwankwaso na zargin cewa wasu sun hada baki da jagororin jam'iyyar APC suna kokarin fakewa da batun rikicin masarautar Kano su tayar da fitina, don gwamnatin tarayya ta samu damar ƙaƙaba dokar ta ɓaci.

Sai dai Fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da zargin da Kwankwason ya yi, tana bayyana shi a matsayin marar tushe ballantana makama.

Fadar shugaban na Najeriya ta bakin ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban ƙasar Abdulaziz Abdulaziz, ta ce sun yi mamakin jin irin waɗannan kalamai da suka fito daga bakin wanda ake yi wa kallon dattijon ƙasa wanda ya rike mahimman mukamai da dama a Najeriya.

"Abun mamaki ne a ce mutum kamarsa ya futo ya yi irin waɗan nan kamalamai, musamman zargin da ya yi na cewar ana son a saka dokar ta ɓaci a Kano ko tayar da rikici a jihar, ko kadan babu ƙanshin gaskiya kan wadannan zarge zarge, kuma a matsayin mu na gwamantin tarayya ba a taɓa yin makamnciyar wannan maganar ba' Inji Abdul Aziz Abdul'aziz

Har Ila yau ya ƙara da cewar batun masarautar Kano al’amari da ke gaban kotu, kuma jami’an tsaro suna bin duk wani umarnin kotu don tsare hakkin kowanne bangare, sannan yace shugaban kasa yana da alaka mai kyau da kowanne bangare.

"Shugaban ƙasa na da alaƙa me kyau da waɗannan mutane biyu da ake taƙaddama a kan su, ba zai yi wani abu da zai kawo cin zarafi ko ace a matsayin sa na shugaban ƙasa, da yake da alhakin kula da kare dukiya da rayukan ƴan Najeriya a ce gwamnatinsa ta yi wani abu irin wanda Rabi'u Kwankwason ya yi zargi ba, don haka mu a ganinmu ya yi kalaman ne don kawai a harzuƙa magoya baya kuma a yi siyasa" inji Abdulaziz

Wannan ce-ce-ku-ce ya kaure ne sakamakon zargin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi na cewar wasu na ƙoƙarin kawo rigingimu a jihar Kano babu gaira babu dalili.

Kwankwason ya ce "dukkan wani mutumin kirki a yau da ke jihar Kano, yana tir da abun da suke faruwa a jihar, a siyasance muna murna, amma a matsayin mu na masu kishin ƙasa, kuma shuwagabanni, muna ganin irin wanaabu babu abin da zai iya haifarwa sai fitintinu.

"Waɗansu ma suna cewa so ake su shigo da fitina shike nan a ɗauki mataki a saka doka akan gwamnatin Kano, amma ina so ku sani suma su sani, dokar da take akasa yanzu ko ka saka dokar state of emergency a jiha, gwamna ya na nan, zai kuma ci gaba da yin aiki, ba wai cire shi za'ai ba, wanna shi ne abinda da dokar ke cewa, kuma doka ce wadda da yawa ba su sani ba, inji Kwankwaso.

'A kai zuciya nesa'

Masu sharhi kan al’amuaran yau da kullum dai, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu inda Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ja hankalin gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Kano da cewa su lura da maslahar al’umma.

"A ko ina sai da zaman lafiya ake iya yin komai, bai kamata a ce gwamantin tarayya ko ta jiha su ringa yin abun da za su tunzura al'amarin ba, illa su zama masu samar da masalaha da zaman lafiya a tsakanin al'ummar su" a cewarsa.

Farfesa Kamilu Fagen ya ce kamata ya yi gwamnatin tarayyar da ta jihar Kano, su lura da cewar ko me ake ciki, su ne shugabanin al'umma, kuma hakki ne da ya rataya a wuyansu da su yi jagoranci wajen kiyaye doka da oda", inji shi.

Wannan rikici kan masarautar Kano dai, ta na ci gaba da daukar hankali a sassan Najierya, inda al’amarin ya rage armashin bikin Babbar Sallah a bana, ko da yake Kanawa na ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum tamkar babu wani zaman tankiya a jihar.

People are also reading