Home Back

Za a Koma Zama a Kotun Koli Kan Shari'ar Gwamnonin Jihohi da Gwamnatin Tarayya

legit.ng 2024/7/5
  • A yau Alhamis ne kotun kolin Najeriya za ta cigaba da sauraron shari'ar da ake yi tsakanin gwamnonin jihohi da gwamnatin tarayya
  • Gwamnatin tarayya ta nemi kotun ta tilastawa jihohi 36 ba ƙananan hukumomin damar juya kasafin kudinsu daga gwamnatin tarayya
  • Sai dai dukkan jihohi 36 sun nuna adawa da kudirin gwamnatin tarayya inda kotu za ta cigaba da sauraron karar a yau Alhamis

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - A yau Alhamis za a cigaba da sauraron kara tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi kan yancin ƙananan hukumomi.

Gwamnatin tarayya ta shigar da gwamnonin jihohi kotu domin a tursasa masu ba ƙananan hukumomi yanci.

Shugaba Tinubu
Za a cigaba da shari'a tsakanin Tinubu da gwamnoni. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito kwamishinan shari'a na jihar Gombe, Zubairu Umar ya ce dukkan jihohi suna adawa da kudirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda zaman kotun baya ya kasance

Bayan gwamnatin tarayya ta shigar da gwamnonin jihohi kotu, gwamnonin sun nuna kin amincewa da abin da gwamnatin tarayya ke bukata.

Biyo bayan kalubalantar kudurin da gwamnonin jihohin suka gabatar, kotun ta bukace su da su gabatar da hujjoji a cikin mako daya.

Martanin da jihohi suka yi a kotun koli

Kwamishinan shari'a na jihar Gombe barista Zubairu Umar ya ce gwamnatin tarayya ba ta da ikon tursasawa jihohi ba ƙananan hukumomin yanci.

Zubairu Umar ya ce duk da cewa shi a jihar sa ba shi da matsalar amma bin doka da oda ya kamata gwamnatin tarayya ta yi.

Dalilin neman yancin ƙananan hukumomi

Gwamnatin tarayya ta ce tana nemawa kananan hukumomi yanci ne biyo bayan rashin amfani da kuɗinsu da jihohi ke yi yadda ya kamata.

Idan kotu ta biya bukatar gwamnatin tarayya, kananan hukumomi za su rika karbar kason kudin wata-wata daga gwamnatin tarayya domin gudanar da ayyuka.

Kwara: An sauke shugabanni ana shirin zabe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya sallami dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 16 a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a yayin da ake shirin gudanar da zabe a jihar,

Asali: Legit.ng

People are also reading