Home Back

Tinubu Na Shirin Sanya Dokar Ta Baci a Kano Domin Kwace Mulki? Gaskiya Ta Fito

legit.ng 2024/7/4
  • Yayin da Rabiu Kwankwaso ke zargin Gwamnatin Tarayya kan rigimar sarautar Kano, fadar shugaban kasa ta yi martani
  • Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya karyata zargin da ake yi na shirin sanya dokar ta baci a Kano domin tuge gwamnati
  • Ya ce kwata-kwata babu wannan shiri inda ya bayyana hakan a matsayin jita-jita kawai masar tushe bare makama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan zargin Sanata Rabiu Kwankwaso game da rigimar sarautar jihar Kano.

Gwamnatin ta karyata zargin Kwankwaso kan cewa tana kokarin sanya dokar ta baci da kawar da gwamnatin Abba Kabir.

Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatarwa The Nation cewa babu kamshin gaskiya a wannan zargi da aka yi.

"Babu kamshin gaskiya kan wannan zargi na Kwankwaso, jita-jita ce kawai ake yadawa."
"Babu yadda za a yi Gwamnatin Tarayya ta sanya dokar ta baci a jiha ba tare da hannun Majalisar Tarayya ba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Majalisar Tarayya yanzu tana hutu babu shugaban kasar da zai tashi kawai ya sanya dokar ta baci a jiha."

- Bayo Onanuga

Wannan na zuwa ne bayan Sanata Rabiu Kwakwaso ya zargi Gwamnatin Bola Tinubu da neman dagula jihar Kano.

Kwankwaso ya zargi gwamnatin ne game da halin da ake ciki yanzu inda ya ce suna jin shawarar makiyan Kano.

Ya ce jami'an tsaron Gwamnatin Tarayya suna nuna goyon baya ga tubabben sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Sanatan ya bayyana haka ne yayin martani kan rigmar masarautun Kano a taron kaddamar da aikin hanya a Madobi.

Kwankwaso ya yabawa Abba Kabir

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya yabawa Abba Kabir wurin kawo ayyukan ci gaba a jihar Kano.

Kwankwaso ya ce gwamnan ya yi kokari duk da tsaiko da wasu makiyan Kano ke kawo masa cikin shekara daya da ya yi.

Asali: Legit.ng

People are also reading