Home Back

NDLEA Ta Cafke Masu Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas

leadership.ng 2024/5/17
NDLEA Ta Cafke Masu Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas

Wani mutum ya yi kashin dauri 80 na hodar ibilis da ya hadiye a cikinsa, lokacin da aka kama shi a filin jirgin saman Legas, yana kan hanyar tafiya kasar Indiya.

Hukumar NDLEA da ke yaki da sha da kuma safarar kwayoyin ta kuma kama wani mai safarar kwayar tare da layu a tashar jiragen ruwan Tincan da ke Legas, inda ta kwace dauri 2,144 na tabar wiwi da ya shigo da ita daga Colorado.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi ya shaida wa manema labarai cewar jami’an hukumar a tashar jiragen saman Murtala sun kama Freeman Charles Ogbonna a wurin da ake gudanar da bincike kafin hawa jirgi, inda aka gano ya hadiye dauri 80 na hodar ibilis.

Babafemi, ya ce an kama Ogbonna wanda yake dauke da fasfo na kasar Liberia ne a ranar 31 ga watan Maris lokacin da yake kokarin hawa jirgin Qatar Airways dauke da sunan Carr Bismark, yayin da bincike ya gano cikakken sunansa Freeman Charles Ogbonna.

Bayan tsare shi a dakin bincike na hukumar, Ogbonna ya yi amai da kuma kashin dauri 80 na hodar da ya hadiye a cikinsa.

Daga bisani wanda ake zargin ya shaida wa NDLEA cewar wani dan uwansa ne ya sanya shi cikin wannan mummunan aikin na hadiye giram 889 na hodar domin safarar ta.

Babafemi ya ce, jami’an NDLEA sun sake kama Imran Taofeek Olalekan dauke da kwaya lokacin da yake kokarin hawa jirgi a tashar Murtala Muhammed zuwa kasar Oman.

Ya ce Imran ya boye kwayar ce a karkashin jakarsa, kuma take aka kama shi.

Har ila yau, ya ce an gano wasu layu da mutanen biyu suka yi amfani da su wajen ganin sun kaucewa jami’an hukumar.

People are also reading