Home Back

NERC Ta Fayyace Wadanda Karin Kudin Wuta Ya Shafa, Ta Yi Karin Haske Kan Samun Wuta

legit.ng 2024/5/17
  • Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya (NERC) ta bayyana yadda tsarin ba da wuta ke kasancewa a faɗin ƙasar
  • Hukumar ta fitar da jadawalin yadda ta ke rarraba wutar ganin yadda ake ta cece-kuce kan karin kudin wutar lantarki
  • Hakan ya biyo bayan ƙarin kudin wutar lantarki a jiya Laraba 3 ga watan Afrilu wanda aka yi korafi kan rashin ingancin wutar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake ta cece-kuce kan karin kudin wutar lantarki a Najeriya, an bayyana yadda gaskiyar abin ya ke.

A jiya Laraba 3 ga watan Afrilu ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da karin kudin wutar a kasar.

Hukumar NERC ta fayyace yawan sa'o'i da ake samun wuta a Najeriya
Hukumar NERC ta fitar da jadawalin yawan sa'o'i da ake samun wuta a Najeriya. Hoto: Nigeria Electricity Regulatory Commission. Asali: UGC

Karin kudin wuta ya jawo kace-nace

Hakan ya jawo ta da jijiyoyin wuya ganin yadda ba a samun wutar a wurare da dama a fadin kasar, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani hukumar rarraba wutar a Najeriya ta yi karin haske kan wadanda karin kudin ya shafa.

Ta ce karin kudin ya shafi wadanda ke rukunin Band A da ke samun wutar akalla na sa'o'i 20 a kowace rana.

Kwastomomi da ke Band A sun samu karin kudin daga N66KwH zuwa N225KwH wanda su ne karin ya shafa.

Jerin yadda ake rarraba wuta a Najeriya

1. Rukunin Band A: su na samun wutar lantarki akalla sa'o'i 20 a kowace rana, kamar yadda NERC ta tabbatar a .

2. Rukunin Band B: su na morar wutar lantarki akalla sa'o'i 16 a rana.

3. Rukunin Band C: Wannan rukuni na samun wutar lantarki akalla sa'o'i 12 a kowace rana.

4. Rukunin Band D: su ne wadanda ke samun wutar lantarki akalla sa'o'i takwas a kowace rana.

5. Rukunin Band E: su ne mafi karancin masu samun wuta akalla sa'o'i hudu a kowace rana.

An kara kudin wutar lantarki

Kun ji cewa Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya, NERC ta tabbatar da kara kudin wutar lantarki a Najeriya.

Mataimakin shugaban NERC, Musliu Oseni shi ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce an kara kudin daga N66/KwH zuwa N225/KwH.

Asali: Legit.ng

People are also reading