Home Back

ƘAWATA GARIN KADUNA: KASUPDA ta fara rushe gine-ginen da a ka yi su ba bisa ƙa’ida ba gadan-gadan a faɗin jihar

premiumtimesng.com 2024/8/22
ƘAWATA GARIN KADUNA: KASUPDA ta fara rushe gine-ginen da a ka yi su ba bisa ƙa’ida ba gadan-gadan a faɗin jihar

Hukumar raya birane ta jihar Kaduna ta fara rushe gine-gine da aka yi su ba bisa ka’ida ba a faɗin jihar.

Kakakin hukumar, Garba Nuhu ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Kaduna.

Garba ya ce, gwamnatin ta bijiro da wannan aiki ne domin kayata jihar ganin wasu sun zo sun mamaye wurare suna kasuwanci a inda aka hana.

Ta kara da cewa, kafin a fara wannan aikin, sai da aka tuntube su aka aika musu da takardu cewa su bar waɗannan wurare.

Wuraren da abin ya shafa sun hada da Unguwan Dosa, Kawo, Mando, Barnawa, Titin Alkali, da dai duk inda aka kafa wuraren dafa abinci da sai da kayan tireda ba bisa ƙa’ida ba.

Sai dai kuma masu wuraren sana’a irin haka sun koka kan bijiro da aiki irin haka a wannan lokaci da ƴan Najeriya ke kuka da tsananin rashin tsaro da fatara.

” Bijiro da aiki irin haka a wannan lokaci ba shi da amfani saboda ana tsananin fama da fatara da kunci da talauci a Najeriya, ɗan inda muke zama mu rufa wa juna asiri kuma gwamnati ta ce mu tsahi, ina talaka zai saka kan shi.

Wani dattijo da ya shekara sama da 20 ya na siyar da kayan Tireda a ire-iren waɗannan wurare ya shaida cewa ba tasa ya ke ji ba, ” idan ni zan iya hakuri, matasa na ke ji ganin yadda komai ya dagule a kasa, ana fama da tsananin talauci.

” Yanzu idan ka kori matashi da ke neman na tuwo a irin wannan wuri ina zai saka kansa. Ga shi ana maganan tsananin rashin tsaro a kasa.

Sai dai kuma duk da korafe-korafen jama’a, hukumar KASUPDA ta ce aikin kawata kaduna shine a gabanta yanzu.

People are also reading