Home Back

RIKICIN DILLALAN FETUR DA KWASTAN: Ƙungiyar IPMAN ta fusata, ta tsaida sayar da fetur a dukkan gidajen mai na Jihar Adamawa

premiumtimesng.com 2024/7/2
Ba a ƙara kuɗin litar mai ba – Kamfanin Mai na Kasa NNPC

Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun tabbatar da cewa Ƙungiyar Dillalan Fetur ta IPMAN, ta kulle dukkan gidajen sayar da fetur na Jihar Adamawa, lamarin da ya haifar da wahala da matsalar zirga-zirgar jama’a, musamman yara da ɗalibai ‘yan makaranta, saboda rashin motoci da baburan sufuri kan tirina.

Wannan mataki na dakatar da sayar da fetur a dukkan gidajen mai na Jihar Adamawa, ya zo ne bayan da IPMAN ta zargi Jami’an Kwastan na Jihar Adamawa cewa su na takura wa maotocin dakon fetur, tare da ƙwace masu fetur a motocin da suke loda wa fetur da gas a jihar, ba bisa ƙa’idar ƙwacewa ba.

Ƙarancin ababen hawa ya haifar da kasa fitar jama’a da dama zuwa wuraren aiki ko sana’a. Sai Keke NAPEP ne ake gani jifa-jifa na karakaina kan titina.

Ma’aikatan gwamnati da dalibai ne lamarin ya fi shafa, kuma su ne suka fi nuna ɓacin ran su.

Sai dai kuma wasu na sukar matakin da IPMAN ta ɗauka, inda suke bada shawarar cewa ya kamata ƙungiyar ta maida hankali kan hana karkatar da fetur, maimakon kulle gidajen mai da ta yi.

A na ta ɓangaren, IPMAN ta haƙiƙice cewa jami’an kwastan a Jihar Adamawa na takura masu, ta hanyar ƙwace masu motoci ɗauke da fetur, ba bisa ƙa’ida ba.

IPMAN dai ta bada gargaɗin wa’adin sa’o’i 72 ga Hukumar Kwastan cewa jami’an ta su kiyaye bin tsarin da doka ta tanadar wajen yin aikin su, gudun kada su janyo IPMAN ta fusata ta tafi yajin aiki.

A yanzu dai jaridu ciki har da Trust sun ruwaito cewa ɗaiɗaikun motoci ake gani kaɗai kan titinan Jihar Adamawa, saboda dakatar da sayar da fetur da IPMAN ta sa aka yi a gidajen mai.

People are also reading