Home Back

Fursunoni da Dama Sun Tsere Daga Gidan Gyaran Hali a Jihar Neja, an Samu Bayanai

legit.ng 2024/5/20
  • Rahotannin da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa fursunoni da dama sun tsere daga gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja
  • Lamarin dai ya faru ne a daren jiya Laraba yayin da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ya lalata katangar gidan yarin
  • Ya zuwa yanzu dai ba a tantance adadin fursunonin da suka gudu ba, amma an tura jami'an tsaro domin kamo wadanda suka tsere

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Suleja, jihar Neja - Wasu fursunoni sun tsere daga gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a daren Laraba.

Fursunoni sun tsere daga gidan gyaran hali na jihar Neja.
Sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya, fursunoni sun tsere a gidan yarin Neja. Asali: UGC

Fursunoni sun tsere daga gidan yari

Ruwan saman da ya mamaye ko'ina a cikin garuruwan Neja da ma makwaftakan garuruwan birnin tarayya Abuja ya lalata wasu sassan katangar gidan yarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa fursunoni da har yanzu ba a tantance adadinsu ba sun yi amfani da damar wajen tserewa.

Wani mazaunin garin Abdullahi Nura ya shaida wa manema labarai cewa fursunonin sun yi galaba a kan jami’an da ke bakin aiki inda suka tsere ta bangarori daban-daban.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin fursunonin sun yi amfani da duwatsu wajen tarwatsa mutanen da suka kawo agaji agaji domin hana su tserewa.

Jami'an tsaro sun dauki mataki

A halin yanzu an baza tawagar jami’an tsaro na hadin gwiwa zuwa cikin garin Suleja domin kamo fursunonin da suka tsere, jaridar Leadership ta ruwaito.

Wani mazaunin garin Suleja, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce:

“Gaskiya ne lamarin ya faru, mun taimaka wajen cafke biyu daga cikin fursunonin, kuma mun mika su ga hukumar gidan yarin."

An kuma tattaro cewa jami’an tsaro na ta harbe-harbe ba a saman iska domin tsoratar da fursunonin da suka tsere su fito daga maboyarsu.

Channels TV ta ruwaito cewa an dan samu nutsuwa yanzu yayin mutane suka ci gaba da gudanar da al’amuran su na yau da kullum yayin da ake ci gaba da neman fursunonin.

Asali: Legit.ng

People are also reading