Home Back

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 715, Sun Ceto Mutane 465 A Watan Afrilu – Hedikwatar Tsaro

leadership.ng 2024/5/19
Sojojin Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 139, Sun Cafke 132 A Cikin Sati 2 —Hedikwatar Tsaro

Hedikwatar tsaron Nijeriya, ta ce, sojojin da aka tura yaki da ‘yan ta’adda a fadin kasar nan sun kashe ‘yan ta’adda 715 sun cafke wasu 146 tare da kubutar da mutane 465 da aka yi garkuwa da su a watan Afrilu.

Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani karin haske kan ayyukan soji.

Janar Buba ya ce, sojojin sun kwato makamai iri-iri 937, alburusai iri-iri 23,034 da kayayyakin sata da darajar su ta haura Biliyan N2,572,397,190.00 a tsawon wannan lokacin.

Daraktan ya kuma jaddada cewa, kudurin da sojojin ke da shi na fatattakar kungiyoyin ‘yan ta’adda ba abu ne da za a tattauna ko a yi sulhu ba a kansu.

Janar Buba ya kara da cewa, a cikin watan sojojin sun gudanar da hare-hare da suka hada da kwanton bauna, kai samame, sintiri na yaki da sauran ayyukan sirri.

Cikin nasara, dukka hare-haren da sojojin suka kaddamar, sun samu nasarar fatattakar ‘yan ta’addan.

People are also reading