Home Back

Jamus da Poland na kokarin karfafa hulda

dw.com 4 days ago
Olaf Scholz na ziyarar a Poland
Olaf Scholz na ziyarar a Poland

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kammala zaman taron zaman taron shawarwari da mahukutan kasar Poland a yayin ziyarar aiki da yake ci gaba da yi a birnin Warsaw.

A yayin taron manema labarai da shugabanin gwamnatoci biyu suka gudanar jim kadan bayan kammala zaman, firaminstan Poland Donald Tusk ya jaddada cewa ya zama dole Jamus ta zama kasar da za ta jagoranci harkokin tsaro a Turai a daidai lokacin da barazanar Rasha ke kara kamari bayan mamayar Ukraine.

Karin bayani: Jamus za ta sa ido kan iyakokinta

Daga nasa bangare shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bukaci samun goyon bayan Poland inda ya ce: 'Hadin gwiwa na kut da kut tsakanin Jamus da Poland na da matukar mahimmanci a garemu.'

Scholz ya kuma da cewa: 'Jamus na bukatar samun goyon bayan Poland a Turai domin aiwatar da manufofinta cikin ra'ayi na rashin son zuciya, wannan kuwa ba zai tabbata ba har sai Poland ta manta da abin rashin dadin da ya faru a lokacin yakin duniya na biyu.

A game da batun tsaro kuwa shugaban gwamnatin ta Jamus ya yi alkawarin cewa: 'A halin da ake ciki batun tsaron Poland batu ne da ya shafi Jamus'.

Karin bayani: Rasha ta katse gas ga Bulgeriya da Poland

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da wani shugaban gwamnatin Jamus ke kai wa Poland a tsawon shekaru shida bayan da gwamnatin masu tsattsauran ra'ayin ta ringa caccakar Berlin saboda mummunan ibtila'in da Jamus ta haddasa wa Poland a lokacin yakin duniya na biyu.

People are also reading