Home Back

Zargin Dokar Bai Wa Auren Jinsi Kariya: Gwamnatin Tarayya Ta Koka Kan Rahoton Wata Jarida

leadership.ng 2024/7/16
Zargin Dokar Bai Wa Auren Jinsi Kariya: Gwamnatin Tarayya Ta Koka Kan Rahoton Wata Jarida

Gwamnatin Tarayya ta koka kan yadda wata jarida wacce ba LEADERSHIP ba ke rahoto abinda ta kira da “rahotannin ƙarya”.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a wani taro da ya yi da manema labarai a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa da ke Abuja a ranar Asabar.

Ya yi jawabi ne sakamakon hayaniyar da ta tashi bayan jaridar ta buga labari cewa, gwamnatin Nijeriya ta rattaba hannu a ƙasar Samoa kan wata yarjejeniya da za ta ba ‘yan luwaɗi da masu maɗigo cikakken ‘yanci a ƙasar nan (Nijeriya).

Labarin ya harzuka jama’a tare da haifar da suka kan gwamnatin Tinubu.

A taron, Minista Idris ya ce gwamnati mai ci yanzu tana mutunta ‘yancin faɗin albarkacin baki da suka mai ma’ana to amma ta damu da “rahotannin ƙarya” da ke fitowa daga jaridar.

Ya ce: “Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnati ce mai kyautata alaƙa da kafafen yaɗa labarai. Hakan ya yi daidai da aƙidar Shugaban Ƙasa a matsayinsa na wanda ya daɗe yana gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya da ‘yancin ɗan Adam.”

Alhaji Idris ya yi nuni da cewa, gwamnati ta ba kafafen yaɗa labarai damar su yi suka da kuma kare ‘yancin faɗin albarkacin baki ga jama’a.

Ya ce, “Amma abin baƙin ciki ne yadda wasu mutane suke wasa da wannan kyakkyawan yanayin wanda gwamnati ta tanadar. Mun yi matuƙar mamakin yawan aikin jarida da kuma kalamai na ganganci da wasu gidajen watsa labarai da mutane suke yi waɗanda suna da illa ga tsaron ƙasa.

“A ganinmu, wannan abin kunya da rashin imani ne domin kuwa babu wannan zancen a cikin takardun da aka sanya wa hannu.

“Abin mamaki, jaridar ba ta ba da wata shaida ba ko ta kawo yarjejeniyar da ta ce an rattaba wa hannu domin kafa hujja.

“Abin baƙin ciki ne a ce labarin maras tushe kuma mai tayar da hankali shi ne wasu limamai suka yi amfani da shi a huɗubarsu bayan an yaudare su da labarin, wanda hakan ya ƙara tunzura jama’a.”

Idris ya ce duk da waɗannan al’amurran, gwamnati za ta bi doka kuma ba za ta ɗauki tsauraran matakai ba.

Ya ce: “Gwamnatocin da suka shuɗe sun rufe gidajen kafafen yaɗa labarai kan abubuwan da ba su kai wannan muni ba, amma mu za mu bi abin a hankali kuma bisa doka.”

Idris ya bayyana cewa gwamnati za ta kai maganar ga Ƙungiyar Mamallaka Gidajen Jaridu ta Nijeriya (NPAN) tare da shigar da ƙara.

Ya ce: “Gwamnatin Tarayya tana goyon bayan kafafen yaɗa labarai masu ɗa’a da faɗin albarkacin baki amma ba za ta amince da labaran ƙarya da ke cutar da zaman lafiya da tsaron ƙasa ba.”

Idris ya halarci taron manema labaran ne tare da Ministan Kasafin Kuɗi Da Tsare-tsaren Ƙasa wanda ya yi ƙarin haske kan yarjejeniyar ta Samoa.

People are also reading