Home Back

An ƙaddamar da aikin gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta a Kano

dalafmkano.com 2024/7/3

Ƙungiyar ma’aikatan lafiya da unguwar zoma ta ƙasa reshen asibitin Ƙashi na Dala a jihar Kano, ta ƙaddamar da aikin gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta ga al’umma.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan lafiya na asibitin Ƙashi na Dala, Kwamared Abubakar Muhammad Isah, ne ya bayyana hakan a wani ɓangaren na tunawa da bikin ranar ma’aikatan jinya ta Duniya, wanda a nan Kano za’a shafe mako guda ana gudanar wa a jihar Kano.

Kwamared Abubakar Muhammad, ya kuma ce sun zaɓi gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta, domin saukakawa al’umma.

A cewar sa, “Mutane ku rinƙa zuwa Asibiti ana gwada lafiyar ku ba sai baku da lafiya za ku je gwaji ba domin mai lafiya shine yake neman magani dan ya yi rigakafi, amma da zarar cuta ta ci karfin mutum to lamarin ya yi munin gaske, “in ji shi”.

Wakilinmu Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar kungiyar za ta kwashe mako guda tana gudanar da taruka dan wayar da kan al’umma a kan batun lafiya.

People are also reading