Home Back

Dalilin da ya sa na garzaya Kotu – Mataimakin Gwamnan Edo da aka tsige

premiumtimesng.com 2024/5/19
Dalilin da ya sa na garzaya Kotu – Mataimakin Gwamnan Edo da aka tsige

Babbar Kotun Tarayya ta aza ranar 19 ga Afrilu, domin fara sauraren ƙarar da tsigaggen Mataimakin Gwamnan Edo, Phillip Shaibu ya shigar, wadda ya ƙalubalanci tsige shi aka yi.

An tsige Shaibu ranar 8 ga Afrilu, bayan Kwamitin Bincike ya kama shi da laifin bayyana sirrin gwamnati.

Majalisar Jihar Edo ce ta tsige shi, shi kuma ya garzaya Babbar Kotun ta Abuja, ya ɗaukaka ƙara.

A ranar Juma’a ce Mai Shari’a Inyang Ekwo ya sa ranar 19 ga Afrilu, domin fara sauraren shari’ar.

Lauyoyin sa ne ciki har da babban lauya Alex Ejesieme sun bayyana a kotun, domin a ba su ranar da za a fara tafka shari’ar.

Shaibu ya shigar da ƙara mai lamba: FHC/ABJ/CS/405/24,

A ranar Alhamis ne dai ya kamata a ce kotun ta fara sauraren ƙarar, amma sai Alhamis aka ce zaman ba zai yiwu ba, saboda kotuna ba su yi aiki ba a lokacin.

“Saboda haka ya mai Shari’a, mun bayyana a kotu a matsayin mu na masu yi wa kotu biyayya.

Bayan tsige Shaibu dai ya ce an cire shi domin kawai a hana shi yin takarar gwamna a PDP.

Lauyan Shaibu mai suna O.A. Gbadamosi ya ce tsigaggen Mataimakin Gwamnan na neman kotu ta haramta ayyana tsigewar, domin kwamitin bincike bai yi masa adalci jin ba, domin ba a saurare shi ba.

Don haka ya ce an tauye masa ‘yanci, haƙƙi bisa yin la’akari da Sashe na 36 na Dokar Najeriya, ta Kundin Dokokin 1999.

Ya ƙara da cewa tsarma wasu mutane uku a cikin kwamitin masu bincike an yi masa rashin adalci, domin shi dai ya san ba za su yi masa adalci ba.

Saboda haka ya nemi mutum huɗu daga cikin kwamitin binciken su cire kan su daga kwamitin, kuma kotu ta haramta kwamitin, sannan a soke tsige shi da aka yi.

People are also reading