Home Back

BA SANI BA SABO: ‘Ko Tinubu da Kashim Shettima za su shiga filin jirgin sama, sai sun biya haraji kafin su wuce – Majalisar Zartaswa

premiumtimesng.com 2024/6/14
Dalilin da ya sa bashi ya yi wa Jiragen Shugaban Ƙasa katutu – Kwamandan Jiragen Shugaban Ƙasa

Majalisar Zartaswa ta amince da wasu ƙa’idojin da ta bijiro da su a taron ta na ranar Talata.

Daga cikin ƙa’idojin, an jaddada cewa daga yanzu duk wanda zai shiga filin jirgin sama na gwamnatin tarayya a ƙasar nan, ko a wane gari ne, tilas sai ya biya haraji a shingen shiga filin jirgin kafin a bar shi ya wuce.

Majalisar Zartaswa ta amince duk wanda zai wuce, ko wane ne, duk muƙamin sa sai ya biya haraji tukunna kafin a bari ya wuce cikin filin jirgin.

“Daga yau ko Shugaban Ƙasa da Mataimakin sa za su shiga filin jirgi, to tilas sai sun biya haraji a daidai shingen karɓar kuɗin haraji na kan titi, kafin su ƙarasa cikin filin jirgin.” Haka aka jaddada tare da amincewar Shugaba Tinubu.

An gudanar da taron makonni biyu kafin cikar Gwamnatin Tinubu shekara ɗaya da kafuwa.

Sauran Batutuwan Da Aka Zartas A Taron Majalisar Zartaswa:

Gwamnatin Tinubu ta kinkimo ayyukan raya ƙasa guda 20, ciki har da sayo tulin motocin sauƙaƙa zirga-zirgam

Gwamnatin Tarayya ta bijiro da ayyukan raya ƙasa guda 20 a zaman da Majalisar Zartarwa ta yi ranar Talata, a Babban Ɗakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa.

Bayan an ɗauki dogon lokaci ana ganawa, a ƙarshe dai an zartas da amincewa kan wasu ayyukan raya ƙasa waɗanda za su bunƙasa tattalin arziki, su jawo masu zuba jari tare da sauƙaƙa hanyoyin gudanar da kasuwanci a cikin ƙasa.

Ayyuka 11 Daga Cikin 20 Da Gwamnatin Tinubu Ta Bijiro Da Su:

1. Shirin ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa da Gidaje na Haɗin-gwiwa (PPP).

2. An jaddda cewa duk wanda ya je Filayen Jiragen Gwamnatin Tarayya sai ya biya haraji kafin ya shiga. Har Shugaban Ƙasa da Mataimakin sa sai sun biya haraji kafin su wuce.

3. An haramta ginar yashi ko rairayi ko ƙasa daga tazarar da ba ta kai nisan kilomita 10 da gadar Gwamnatin Tarayya ba.

4. Gwamnatin Tarayya ta bada wa’adin makonni huɗu a sauya fasalin bayar da bizar gaggauta bai wa baƙi masu kawo ziyara da harkokin kasuwanci damar shigowa Najeriya.

5. Za a gina tashoshin hawa da sauka motocin haya a Kugbo, Abuja Central Area da Mabushi duk a FCT, kan kuɗi Naira biliyan 51, a cikin watanni 15.

6. Za a gina Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, kan kuɗi Naira biliyan 37.2.

7. An amince Hukumar Kwastan ta sayo motoci Toyota Land Cruiser Buffalo guda 200, kan kuɗi Naira biliyan 12.5. Kuma su kasance ba masu amfani da fetur ba.

8. An amince a cire Naira tiriliyan 1.6 domin fara aikin titin Legas zuwa Kalaba.

9. An amince da bada kwangilar gyaran titin Koton-Ƙarfe zuwa Abaji, kan titin Abuja zuwa Lokoja, kan kuɗi Naira biliyan 89.

20. An bada kwangilar gina titin by-pass a Kano, kan kuɗi Naira biliyan 230. Aikin mai tsawon kilomita 37, zai ƙunshi har da gina gadoji da gadojin sama masu yawa.

11. An amince da kwangilar aikin titin Sokoto-Illela-Badagry. Wanda ake sa ran zai haɗe da titin Legas zuwa Kalaba.

People are also reading