Home Back

Gwamna Ya Fadi Dalilin Kin Fara Sabon Aiki a Jiharsa Bayan Shekara 1 a Mulki

legit.ng 2024/7/3
  • Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya yi magana kan shekara ɗaya da ya kwashe a kan kujerar mulkin jihar
  • Gwamnan ya bayyana cewa ya gaji kwantan ayyuka masu yawa da ba a kammala ba daga gwamnatocin da suka gabata
  • Ya bayyana cewa hakan ya sanya bai ba da sababbin kwangiloli ba a jihar tun bayan hawansa kan mulki shekara ɗaya da ta gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya koka kan yadda gwamnatocin baya suka bar wasu ayyuka da ba a kammala ba a sassan jihar.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta ga buƙatar bayar da sababbin kwangiloli ba a cikin shekarar da ta gabata saboda ya fara aiki domin kammala ayyukan da aka bari domin amfanin al'umma.

Gwamna Mutfwang bai ba da sababbin kwangiloli ba a Plateau
Gwamna Caleb Mutfwang ya cika shekara 1 kan mulkin Plateau Hoto: Caleb Mutfwang Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da yake ganawa da ƴan jarida a Jos a wani ɓangare na gudanar da bukukuwan cika shekara ɗaya kan karagar mulki, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya kuma ce ba adalci ba ne a bayyana kashe-kashen da ake yi a jihar a matsayin rikicin Fulani da Manoma, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Me ya hana Gwamna Caleb ba da kwangila?

Gwamnan ya yi nuni da cewa gwamnatinsa s koda yaushe za ta ɗauki matakai ne domin amfanin jihar da al’ummar da suka zaɓe shi kan karagar mulki

"A cikin shekarar da ta gabata, abin da muka yi ƙoƙarin yi shi ne daidaita al'amura. Ba mu je ko'ina cikin abin da muke so mu yi ba."
"Ba mu bayar da sababbin ƙwangiloli ba. Abin da muka yi ƙoƙarin yi shi ne duba kwangilolin da aka bayar saboda mun fahimci cewa ƙyale ayyukan da ba a kammala ba abu ba ne mai kyau ga asusun jiha."
"Mun yi imanin cewa gwamnati ci gaba ce kuma ko da ba ka son gwamnatin da ta wuce, kana da haƙƙi a kan jama'a domin ci gaba da abin da zai amfanar da su."

- Caleb Mutfwang

An buƙaci gwamnan Plateau ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa an buƙaci Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato da ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC domin ya kara samun daraja a idon al'umma.

Kungiyar APC ta Arewa maso tsakiya ce ta yi wannan kiran a Jos, babban birnin jihar Filato, a wajen taronta na farko na shekarar 2024.

Asali: Legit.ng

People are also reading