Home Back

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 640 sun kama 1,051 cikin watan Mayu

premiumtimesng.com 2024/7/1
TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

Hedikwatar Tsaron Sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta kashe ‘yan ta’adda 640 tare da damƙe wasu 1,051 a cikin watan Mayu. Kuma ta ceto mutanen da aka yi garkuwa da su har mutum 563 duk a cikin watan Mayu.

Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Edward Buba ne ya bayyana haka yayin da ya ke wa manema labarai ƙarin bayani, ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce wasu manyan kwamandojin Boko Haram da mayaƙan su duk an karkashe su, lamarin da ya ce wannan nasara ta rage ƙarfin ‘yan ta’adda sosai da sosai.

Manjo Janar Buba ya ce an kama wasu masu kai wa ‘yan ta’adda kayan amfanin yau da kullum da kuma masu yi masu infoma.

Ya ce sojojin Najeriya sun kuma ƙwato makamai 707 da albarusai 16,487 duk a cikin watan Mayu.

Idan ba a manta ba, cikin makon jiya ne Ministan Harkokin Tsaro, Muhammad Badaru ya bayyana cewa a cikin shekara ɗaya sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga 9,300, sun kama kimanin 7,000 kuma sun ceto mutum 4,641 duk a cikin shekara ɗaya.

People are also reading