Home Back

Mun ƙudiri aniyar gyara tarbiyyar Matasa a jahar mu – Gwamnatin Kano

dalafmkano.com 2024/5/20

Gwamnatin Kano tasha alwashin ci gaba da magance matsalar tsaro musamman wajen kawo karshen kwacen waya da harkar Daba da ake fama dashi a jihar kano.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya bayyana hakan a yayin karɓar baƙuncin mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, a fadar fadar gwamnatin Kano, a wani ɓangare na bikin hawan Nassarawa, da ya gudana a yau Juma’a.

Abba Kabir, ya kuma ce duk da matsalolin da gwamnatin Kano ta fuskanta a baya na harkar shari’a, amma hakan bai hana ta cika alkawarin da ta ɗauka ga al’ummar jihar kano a yakin neman zaben shekarar 2023 da ta gabata ba.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba ta tsaya ba sai da ta yi kokarin magance matsalar da harkar Ilimi ke fama dashi wajen gyara makarantu da fitar da ɗalibai kasahen waje dan karo Ilimi kyauta.

“Gwamnatin mu ta bijiro da tsarin tallafawa masu harkar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da harkar Daba, da sana’oin dogaro da kai domin kawo karshen Daba a jihar kano, “in ji Gwamna Abba Kabir”.

Hawan Nasarawa dai hawa ne da ake sada zumunci a tsakanin masarautar Kano da gwamnatin Jihar Kano, da kuma al’ummar jihar, wanda da aka saba gudanar da shi a duk rana ta uku, na bikin ƙaramar Sallah, da Babba.

Da yake jawabi tunda farko mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yabawa gwamnatin Kano akan tsarin da ta fito dashi na ciyar da al’ummar jihar kano gaba, musamman ma tsarin ciyarwar azumi da tayi ga mabukata a watan Ramadan da ya gabata.

Ya ci gaba da cewa, “Wannan ciyarwar ga al’umma tsari ne da ya kamata ya ɗore domin rage raɗaɗi da yunwa da ake fama da ita; muna shawartar Gwamnatin Kano, da ta saka ido sosai wajen kawo ƙarshen Daba da ƙwacen waya da hawa doki ana sukuwa ba bisa ka’ida ba, “in ji Sarkin”.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito mana cewa, Sarkin ya kumashawarci gwamnatin Kano, da ta ƙara dagewa wajen ci gaba da tallafawa Ilimin ɗalibai da ke fadin jihar kano, da sauran ayyuka da za su kawo wa jihar kano ci gaba.

People are also reading