Home Back

Gwamna Dauda Ya Karrama Jami'an Rundunar Askarawan Zamfara, Ya Yi Musu Sabon Alkawari

legit.ng 2024/7/2
  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba da ƙwazon da jami'an tsaro na rundunar Askarawan Zamfara suke nunawa a wajen yaƙi da ƴan bindiga
  • Gwamnan ya karrama wasu jami'an rundunar mutum 20 saboda jajircewarsu wajen ganin an kawo ƙarshen ayyukan masu tayar da ƙayar baya
  • Dauda Lawal ya kuma yi alƙawarin kula da dukkanin buƙatun iyalan jami'an rundunar da suka rasa ransu a bakin aiki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya karrama jami’an tsaro 20 na rundunar CPG wacce aka fi sani da Askarawan Zamfara.

Gwamna Dauda ya ba su lambobin yabo ne saboda ƙwazon da suka nuna kuma ya yi alƙawarin tallafawa iyalan waɗanda suka mutu a wajen yaƙi da ƴan bindiga.

Dauda Lawal ya karrama jami'an tsaro
Gwamna Dauda ya karrama jami'an rundunar Askarawan Zamfara Hoto: @daudalawal Asali: Twitter

An karrama jami'an Askarawan Zamfara

Gwamnan ya karrama su ne a gidan gwamnati da ke birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Asabar, ta bayyana cewa jami'an tsaron da aka karrama sun taka rawar gani sosai.

Kwamandan rundunar Askarawan Zamfara, Birgediya Janar Lawal Bature Mohammed, shi ne ya jagoranci jami'an tsaron da aka karrama zuwa gidan gwamnati.

Wane alƙawari Gwamna Dauda ya yi?

A yayin jawabinsa wajen karrama jami'an tsaron da aka yi a ranar Alhamis, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada shirin gwamnatinsa na kula da jin daɗin Askarawan.

"Ku ɗauki karramawar da aka yi muku a matsayin hanyar ƙara muku ƙarfin gwiwar ci gaba da wannan muhimmiyar sadaukarwar da kuke yi."
"Ba za mu iya biyan ku ba kan aikin da kuke yiwa jiha da al'umma, abin da kawai za mu iya yi shi ne mu ƙara muku ƙarfin gwiwar ci gaba da nuna ƙwazo."
"Ina ba ku tabbacin cewa ina da shiri mai kyau a kan iyalan jami'an CPG da suka rasa ransu a bakin aiki. Za mu kula da dukkanin buƙatunsu sannan mu ba su tallafin da ya dace."

- Dauda Lawal

Gwamna Dauda ya fara biyan sabon albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000 ga ma’aikata a jihar da ke yankin Arewa maso Yamma.

Hakan ya biyo bayan alƙawarin da Gwamna Dauda Lawal ya ɗauka yayin ganawa da shugabannin ƴan kwadago a jihar domin fara biyan sabon alwashin ga ma'aikatan.

Asali: Legit.ng

People are also reading