Gwamna Dauda Ya Karrama Jami'an Rundunar Askarawan Zamfara, Ya Yi Musu Sabon Alkawari
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya karrama jami’an tsaro 20 na rundunar CPG wacce aka fi sani da Askarawan Zamfara.
Gwamna Dauda ya ba su lambobin yabo ne saboda ƙwazon da suka nuna kuma ya yi alƙawarin tallafawa iyalan waɗanda suka mutu a wajen yaƙi da ƴan bindiga.
Gwamnan ya karrama su ne a gidan gwamnati da ke birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Asabar, ta bayyana cewa jami'an tsaron da aka karrama sun taka rawar gani sosai.
Kwamandan rundunar Askarawan Zamfara, Birgediya Janar Lawal Bature Mohammed, shi ne ya jagoranci jami'an tsaron da aka karrama zuwa gidan gwamnati.
A yayin jawabinsa wajen karrama jami'an tsaron da aka yi a ranar Alhamis, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada shirin gwamnatinsa na kula da jin daɗin Askarawan.
"Ku ɗauki karramawar da aka yi muku a matsayin hanyar ƙara muku ƙarfin gwiwar ci gaba da wannan muhimmiyar sadaukarwar da kuke yi."
"Ba za mu iya biyan ku ba kan aikin da kuke yiwa jiha da al'umma, abin da kawai za mu iya yi shi ne mu ƙara muku ƙarfin gwiwar ci gaba da nuna ƙwazo."
"Ina ba ku tabbacin cewa ina da shiri mai kyau a kan iyalan jami'an CPG da suka rasa ransu a bakin aiki. Za mu kula da dukkanin buƙatunsu sannan mu ba su tallafin da ya dace."
- Dauda Lawal
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000 ga ma’aikata a jihar da ke yankin Arewa maso Yamma.
Hakan ya biyo bayan alƙawarin da Gwamna Dauda Lawal ya ɗauka yayin ganawa da shugabannin ƴan kwadago a jihar domin fara biyan sabon alwashin ga ma'aikatan.
Asali: Legit.ng