Home Back

Kamfanin barasar Najeriya ya ce zai rufe 2 daga cikin cibiyoyin sarrafa giyarsa

rfi.fr 2024/5/3

Najeriya ā€“ Katafaren kamfanin sarrafa barasar Najerya da ake kira 'Nigerian Breweries' ya sanar da cewar zai yi garambawul a kan ayyukan da yake yi, wanda zai kai ga rufe cibiyoyi guda 2 daga cikin 9 da yake yin giyar saboda karancin kudade da kuma hauhawan farashin kayan aiki.

Wallafawa ranar: 19/04/2024 - 17:59

Minti 1

Katafaren kamfanin sarrafa barasar Holland dake yin giyar Heineken
Katafaren kamfanin sarrafa barasar Holland dake yin giyar Heineken AFP/File

kamfanin ya bayyana wasu daga cikin matsalolin da yake fuskanta da suka hada da karancin kudaden kasashen ketare da kuma asarar da yake tafkawa.

kamfanin yace a bara ya yi asarar kudaden da suka kai sama da naira biliyan 153 wanda shine mafi muni a cikin shekaru 77 da ya kwashe yana aiki a Najeriya.

Kamfanin sarrafa barasar yace kusan rabin kudin da yake kashewa ana amfani da su ne wajen sayo kayan aiki daga kasashen ketare, abinda ya sa matsalolin tattalin arzikin da aka fuskanta a Najeriya ya sanya shi asarar naira biliyan 106.

shugaban kamfanin Hans Essaadi yace tuni kamfanin ya sanar da aniyar ta sa na rufe 2 daga cikin kamfanonin da kuma rage ma'aikata ga kungiyoyin ma'aikatan dake masa aiki, yayin da yace babu makawa zai sallami wasu daga cikin ma'aikatansa.

Esssaadi yace sun shirya yadda zasu rage radadin sallamar ma'aikatan wajen basu kudaden sallama mai tsoka da kuma tallafi.

People are also reading