Home Back

Kotu Ta Yanke Hukuncin Daurin Watanni 6 Kan Shararren Dan Daudu, Bobrisky

legit.ng 2024/5/17

Jihar Legas - Babbar kotun tarayya da ke zam aa jihar Legas ta yanke wa fitaccen ɗan daudun nan, Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky hukunci ranar Jumu'a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kotun ta yanke wa shahararren ɗan daudun hukuncin ɗauri a gidan gyaran hali na tsawon watanni shida ba tare da zaɓin tara ba.

Mai shari'a Abimbola Awogboro na babbar kotun tarayya ne ya yanke wa ɗan daudun wannan hukunci ranar 12 ga watan Afrilu, 2024, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tun makon jiya dai ake tsare da Bobrisky gabanin yanke masa hukunci bayan ya amsa aikata laifukan da ake tuhumarsa da su.

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ce ta gurfanar da fitaccen ɗan daudun kan tuhume-tuhume guda 6.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading