Home Back

Raya Karkara: Gwamnatin Kano Za Ta Kashe N2.6bn a Gina Titi Mai Nisan 14.7km

legit.ng 2024/7/3
  • Gwamnatin jihar Kano za ta gina tituna biyu masu nisan kilomita 7.2 da 7.5 wadanda za su lakume Naira biliyan 2.6
  • Wannan na daga shirin gwamnatin Kano na gina titunan karkara a garuruwa 10 da ke mazabun tarayya uku na jihar
  • Gwamna Abba Yusuf wanda ya bayyana hakan a ranar Juma'a ya ce ya himmatu wajen inganta rayuwar mazauna karkara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce ya kaddamar da fara gina titin karkara mai nisan kilomita 7.2 daga Mil Goma zuwa 'Yankatsari.

Abba ya kaddamar da ginin tituna a Kano
Kano: Abba ya kaddamar da ginin titunan N2.6bn a garuruwan karkara. Hoto: @Kyusufabba Asali: Twitter

Abba zai bunkasa garuruwan karkara

Haka zalika, Gwamna Abba Yusuf ya kuma kaddamar da gina wani titin mai nisan kilomita 7.5 na hanyar garin Rijiyar Gwangwan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda ya sanar da hakan a shafinsa na X a safiyar ranar Juma'a, Abba Yusuf ya ce gwamnatin Kano za ta kashe Naira biliyan 2.6 wajen aiwatar da aikin.

Gina titunan na daga cikin shirin gwamnatin Kano na gina titunan karkara a garuruwa 10 da ke mazabun tarayya uku na jihar.

Gwamna Yusuf ya ce gwamnati za ta gina akalla kilomita 70 na tituna a wadannan garuruwa.

Hadin guiwar gwamnati da masu zuba jari

A cewar gwamnan Kano:

"Gwamnatin Kano za ta aiwatar da ginin titunan ne tare da hadin guiwar bankin raya Musulunci (ISDB) da asusun tallafawa rayuwar al'uma (LLF).
"Za a gudanar da shirin ne karkashin kulawar hukumar noma da raya karkara ta Kano (KNARDA) ta hannun shirin raya noma da kiwo na jihar (KSADP)."

Gwamnatin Kano ta himmatu wajen aiwatar da ayyukan da za su samar da ababen more rayuwa ga al’ummomin karkara a jihar.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Abba ya biya wa dalibai kudin NECO

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf ya fitar da Naira biliyan 2.9 domin biya wa ɗalibai 119,903 na Kano kudin jarabawar NECO da NBAIS ta 2024.

Kwanishinan ilimi na jihar Kano, Dakta Umar Doguwa ya bayyana hakan a ranar Alhamis yana mai cewa Gwamna Yusuf na da burin 'yayan talaka su yi karatu mai zurfi.

Asali: Legit.ng

People are also reading