Abubuwan da Ya Kamata Duk Mai Niyyan Layya Ya Kiyaye a Kwanaki 10 Kafin Sallah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Bayan ganin wata a jiya Alhamis, yau an wayi gari 1 ga watan Zul Hijja kamar yadda mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya sanar.
Daga cikin ayyukan ibada da al'ummar Musulmi suke gabatarwa a watan Zul Hijja akwai layya da ake farawa ranar 10 ga wata.
A wani bidiyo da Mika'il Abubakar Yyg ya wallafa a shafin Facebook, malam Umar Shehu Zariya ya bayyana abubuwan da ake so wanda zai yi layya ya nisanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malam Umar Shehu Zariya ya bayyana cewa dukkan wanda ya yi niyyar layya to dole ya nisanci yanke farce da zarar wata ya kama.
Malamin ya kara da cewa haka hukuncin yake idan mutum ya yi niyya a lokacin da babu kudi a hannunsa amma yana tsammanin samunsu a karshen wata.
Har ila yau malamin ya bayyana cewa bai kamata ga duk wanda zai yi lahiya ya yi aski ba, yin aski kuma ya kunshi aske duk wani gashi a jikinsa.
Malam Umar Shehu Zariya ya ce la'alla hikimar sanya dokokin ita ce koyawa Musulmi zaman hakuri da kuma shirin zaman kabari tunda a can babu yanke farce da aski.
A wani bangare kuma, Sheikh Muhammad Salih Al-Munajjid ya kara da cewa ana so mutum ya nisanci yanke duk wata fata ko sashen jikinsa da zarar ya yi niyyar layya.
Sheikh Muhammad Salih Al-Munajjid ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Islamqa da yake amsa tambayoyi.
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe ta sanar da canza salon yadda tsarin almajiranci ke tafiya wajen shigo da tsare-tsaren zamani.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mai ba gwamnan jihar shawara kan harkar tsangaya da almajiranci, Aminatu Sheikh Dahiru Usman Bauchi ce ta fadi haka.
Asali: Legit.ng