Home Back

Dakarun Sojoji Sun Yi Nasara Kan 'Yan Ta'adda a Jihohin Katsina da Plateau

legit.ng 2024/5/17
  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi artabu da ƴan ta'adda a garin Danmusa, hedkwatar ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Katsina
  • A yayin ƙazamin artabun sojojin sun hallaka ɗan ta'adda ɗaya tare da ƙwato makamai masu tarin yawa da babur guda ɗaya
  • A wani samame na daban kuma, sojojin sun ceto wasu mutum biyu da ƴan ta'adda suka yi garkuwa da su a jihar Plateau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Dakarun sojojin Najeriya sun kashe wani ɗan ta’adda a Katsina tare da kuɓutar da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a jihar Filato a wani samame daban-daban.

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin ta fitar a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

Sojoji sun hallaka dan ta'adda
Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda Hoto: HQ Nigerian Army Asali: Facebook

Sojoji sun fafata da ƴan ta'adda

Sanarwar ta ce dakarun sojojin tare da tawagar ƴan sanda da jami'an rundunar tsaron jihar Katsina, sun yi artabu da ƴan ta'adda a garin Danmusa hedkwatar ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce, a yayin ƙazamin artabun da sojoji suka yi da ƴan ta’addan, sun yi nasarar kashe dan ta’adda ɗaya tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, harsasai guda biyu masu kaurin 7.62 mm da kuma babur.

Sojojin sun kuma gano wata jaka ɗauke da jigida guda huɗu da babu komai a ciki da kuma abin caji, wanda ake amfani da shi wajen sadarwa da abubuwa masu fashewa.

Sojoji sun ceto mutum biyu

A wata arangama ta daban, dakarun sojojin bayan samun kiran gaggawa kan satar mutane a kan hanyar Maraban-Jema’a a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau, sun ceto mutum biyu da aka sace.

A cewar sanarwar masu garkuwa da mutanen sun tsere ne bayan sun hango sojojin inda suka bar mota ƙirar Peugeot 307 da mutum biyun da suka sace.

Sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun hallaka ƴan ta'adda bakwai a jihar Sokoto.

Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka tsagerun ƴan ta'addan ne a yankin Modachi na ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

People are also reading