Home Back

HAJJI 2024: Cikin awa 24, Najeriya ta rasa Alhazai biyu a Makka

premiumtimesng.com 2024/6/26
HAJJI 2024: Cikin awa 24, Najeriya ta rasa Alhazai biyu a Makka

Cikin awa 24 alhazai biyu daga jihar Kebbi sun rasu a dalilin fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin rasuwar mahajjacin na farko wanda shima ya yi fama ne da ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Shugaban hukumar Alhazai na Jihar Kebbi Faruku Aliyu-Enabo ya sanar da rasuwar mahajjacin na biyu ranar Lahadi inda shima ya ce ya yi fama ne da gajeruwar rashin
lafiya.

” Wanda ya rasu mai suna Muhammad Suleiman, ɗan asalin jihar Kebbi ne. Ya rasu bayan fama da ya yi da ƴar gajeruwar rashin lafiya.

” Tuni dai an suturtashi a Makka, sannan kuma ina mika ta’aziyya ta ga ƴan uwansa da Iyalansa. Muna rokon Allah ya sa Aljanna ce makomarsa ya ji kan sauran bayin Allah da suka rasu Amin.

Jihar Kebbi ce jihar farko da aka fara jigilar maniyyatan ta.

Zuwa yanzu hukumar NAHCON ta kwashe maniyyata 20,974 daga Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki.

People are also reading