Back to the last page

'Ƴan ƙasata Afghanistan na buƙata ta fiye da ko yaushe'

bbc.com 21 hours ago

Asalin hoton, Zarifa Ghafari

Zarifa Ghafari
Bayanan hoto, Zarifa Ghafari ta saba da shiga lungu da saƙo na inda maza suka mamaye a Afghanistan

“Afghanista ƙasata ce. Idan ban koma na taimaka wajen sake gina ƙasata ba wa zai yi?” Tambayar da wata ‘yar siyasa mai kuma rajin kare hakkin mata, Zariga Ghafari, ƴar shekara 28 kenan ke yi.

A lokacin da take da shekara 24 ta kasance matashiya mafi ƙarancin shekaru mace da ke riƙe da muƙamin magajiyar gari a Afghanistan. Tun bayan wannan lokaci, tana rayuwa a Jamus.

‘Yan Afghanistan da dama sun bar kasar ba tare da sake dawowa ba. Amma a farkon wannan shekara, Ghafari ta yanke shawarar ziyartar Afghanistan inda yanzu take kokwanton komawa kasar.

Ghafari ta tattauna da BBC daga Jamus kan rayuwarta, takaitacciyar ziyarar da ta kai Afghanista da Taliban ke mulka da kuma burikanta.

Asalin hoton, Zarifa Ghafari

Zarifa Ghafari
Bayanan hoto, Taliban ne suka kashe baban Zarifa Ghafari

“Ni baƙuwa ce a Jamus. Zan koma gida da zarar na gama aikina,” a cewarta.

Tana tallata littafinta da wani shirin talabijin a kan rayuwarta, da wani shafi ke wallafawa.

”Ban damu da tattaunawar da ake yi da ni ba a ciki da wajen ƙasashe. Abu mafi muhimmanci shi ne na kasance da al’ummata a ƙasata. Ina son na raba duk abin da na mallaka da ‘yan kasata Afghanistan,” kalamanta kenan a tattaunawarta da BBC.

An haifi Ghafari a shekarun 1990, lokacin yaƙin neman iko da ya kai ga janyewar Tarayyar Soviet.

Ta yi rayuwa a lokacin mulkin Taliban na farko da gwamnatin da Amurka ke mara wa baya.

Lokacin da take da shekara 16, ta samu cikakken tallafin karatu inda ta je Indiya domin karantar kimiyyar tattalin arziki da siyasa.

Shekarunta biyu a Indiya, Ghafari ta gamu da haɗari mota a ƙoƙarin tsallaka titi. Ta shafe tsawon shekara 25 cikin yanayi na dogon suma.

Asalin hoton, Zarifa Ghafari

Zarifa Ghafari
Bayanan hoto, Gruesome killing of a young woman fired up Ghafari to grow interest in politics

A lokacin da take kwance a asibiti, sai ta fara sha’awar harkokin siyasa. A wannan lokaci ana zanga-zanga kan kazamin kisan da aka yi wa wata mata – Farkhunda Malikzada – da aka lakadawa duka har mutuwa a Kabul bayan an zargeta da kona Al-Kur’ani.

Ghafari ta kadu sosai. Bayan an sallameta daga asibiti, sai ta shiga zanga-zanga. An soma diga mata dandanon mulki a 2018, lokacin da aka zabeta a kujerar magajiya. Mukamin da ta rike na tsawon shekara uku.

A ranar farko na kama aiki, dukkanin maza abokan aikinta sun fice daga ginin ofishin, a cewarta.

"Na gayyaci kowa taro inda na shaida musu cewa duk mai son aiki a karamar hukumar birni su koma aikinsu. Duk mutumin da bai fito ba, zan sanar da gwamnatin Tarayya,” ta fitar da gargadi.

Wannan barazana tayi aiki. A matsayin magajiyar gari, ta kasance cikin hada-hada ayyukan kula da gine-gine haramtattu a birnin. Ta tabbatar da cewa shaguna na biyan kudaden haraji. Ta kuma jagoranci gangami domin tsaftacce muhalli. Ghafari ba ta mukami a karamar hukumarsu a yanzu.

Bayan rushewar gwamnatin da Amurka ke marawa, ta tsere kasar tare da iyayenta zuwa Jamus. Amma zuciyarta na tare da Jamus.

“Na kalubalanci kai na cikin gwagwarmaya inda na soma tattaunawa a tarukan fadin Turai. Ina kokarin jan hankalin duniya ga rikicin Afghanistan.”

Ghafari ta yi ƙoƙarin tara kudi tare da farfado da shirin horar da mata a Kabul.

Ta shiga fafutika lokacin da ta karanta rahotanni labaran iyalan da ake cewa suna tilastawa yara mata aure domin samun kudin sadakin rayuwa.

Akalla ta yi kokarin hana aure biyu ta hanyar shiga tsakani da samar da kudi ga iyalan da ke cikin talauci.

Asalin hoton, Zarifa Ghafari

Zarifa Ghafari
Bayanan hoto, Ghafari ta kai ziyara wani kauye inda ta ji damuwowinsu

Ta yanke wata shawara ta bambarakwai a watan Fabarairu. Ta shirya kai ziyara Afghanistan.

Ghafari ta dan soma taka tsan-tsan kan a kama ta. Ta tuntubi kakakin Taliban wanda ya tabbatar mata da cewa ba za ta fuskanci tsangwama ba. Ghafari ta ƙi bude ciki ta yi bayyani sosai kan dalilanta na komawa gida.

Ta kuma musanta wasu labarai da ake wallafawa a shafukan sada zumunta cewa ‘ta kulla yarjejeniya da mayakan’. Babu wani fitaccen dan siyasa a Afghanistan da ke zaman hijira da ya amince da wannan zargi.

‘Ziyarar da na kai wanda ya shafe ni ne kai tsaye. Ba ta da alaka da Taliban,’ a cewarta.

Da rakiyar tawagar masu daukar hoto ta ziyarci garinsu kai tsaye Maidan Shahr, mai tazaran kilomita 40 da kudu maso yammacin Kabul.

“Na ziyarci kabarin mahaifina, na shafe sa’o’i ina kuka. Na fada masa damuwata ta kadaici da raba ni da gidanmu,”

Mahaifinta tsohon jami’in soja ne a Afganistan. Mayakan Taliban ne suka kashe shi a 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Zg
Bayanan hoto, Ghafari has survived several assassination attempts including a suspected gas leak at her home - due to which she still has scars in her hand

Tana taka tsan-tsan da munanan abubuwan da ka iya faru, saboda munanan hare-haren da suka sha rutsaw da ita a baya. A lokacin da ta je ziyarar ko yaushe Ghafari na tafiya duk inda za ta je ne ƙarƙashin rakiyar ƙanin mahaifiyarta.

"Na haɗu da marayu da matan da mazajensu suka mutu da mata da maza. Na yi magana da yara matan da aka tilasta wa barin makaranta da masu aiki a kafafen yada labarai.

"Mata da yawa sun yi magana ne kawai a kan ƙarancin abinci."

Ghafari ta tuna da yadda ta sha mamakin ganin yadda wasu maza suka yi maraba da ita a gundumar Day Mirdad.

Zarifa Ghafari

Asalin hoton, Zarifa Ghafari

Babu wuta da tsarin zubar da shara a yankin.

"Suna so su inganta asibitin da ke wajen da kuma faɗaɗa da sake buɗe makarantar ƴan mata."

"Wasu maza da ba sa ma iya zama su tattauna da matansu kuma ba sa sauraron kowace mace sai ga su suna min magana a kan abubuwan da suka shafi mata."

"An yi ganawar ce a wani gini da aka dasa tutar Taliban a kansa."

Asalin hoton, Zarifa Ghafari

Zarifa Ghafari
Bayanan hoto, Ghafari visited to her father's grave too when she was back for a short trip.

Kafin Ghafari ta zama magajiyar gari sai da ta yi aiki a matsayin ƴar jarida tare da samar da gidan rediyon da ke mayar da hankali kan ƙarfafa mata. Mutane da dama da ta sani a baya duk sun je ganin ta.

Sa'o'i kaɗan kafin ta bar Afghanistan ta amince da nadar wata hira da ita a wani gidan talabijin. Ta yi kira da a kawo ƙarshen rikice-rikice.

"Idan Taliban ta yi alkawarin ba za ta kashe mutane ba, to ba za a dinga samun yara marayu barkatai ba," ta shaida wa gidan talabijin ɗin, "Kuma ni ma zan yafe musu.

Ta ga yadda tsaro da ƴancin ɗan adam da suka danganci mata sun taɓarɓare sosai a kasar a ziyarar ƙrshe da ta kai ta ƙarshe.

Kwanan nan aka haramta wa mata zuwa wuraren wasanni. Kuma a yanzu ana yanke tsauraran hukunci da suka haɗa da yanke hannu ga wasu laifuka.

Asalin hoton, Marcel Mettelsiefen

Ghafari says she left the country last year primarily due to concerns over her siblings' education
Bayanan hoto, Ghafari says she left the country last year primarily due to concerns over her siblings' education

Ghafari is preparing to live in the Taliban ruled country.

"I am not waiting for the ground to get levelled. I want to be with my people in these difficult times. I want to work for them while I am young and have the energy."

"I became famous because of my country and my people. People are important, not the government," she continues. "I learnt from my last trip that our country needs people like me more than ever."

Ghafari also stresses the importance of education for women and girls. "If the girls of today are not educated, how are we going to get educated mothers tomorrow?"

But she is hopeful that there will be a turnaround of fortune.

"The cruelty and tyranny will not last long."

Back to the last page