Home Back

RANGADIN DUBA NOMAN SHINKAFA A JIGAWA: Muna sa ran samun tan miliyan 1.6 na shinkafa cikin wannan shekarar – Gwamna Namadi

premiumtimesng.com 2024/6/16
RANGADIN DUBA NOMAN SHINKAFA A JIGAWA: Muna sa ran samun tan miliyan 1.6 na shinkafa cikin wannan shekarar – Gwamna Namadi

A ci gaba da rangadin sa na Dubagarin yadda noman shinkafa ke tafiya, Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya bayyana cewa ya na farin cikin ganin yadda noman shinkafa ta hekta 200,000 ke tafiya a faɗin jihar, wanda ya ce zai rage matsalar ƙarancin abinci sosai a faɗin ƙasar nan.

“A nan yau, ina jin na fi kowa farin cikin ganin yadda aikin noman nan ke tafiya. Saboda na yi rangandin gonakin noman shinkafar nan a Jigawa, kuma a hasashen da muka yi, ana noman shinkafa da ta kai kadada 200,000 a jihar nan.

“To kun ga da waɗannan kadada 200,000 za a iya tan 800,000 na shinkafa. Hakan kuwa ai shinkafa ce mai tarin yawa a Najeriya.

“Sannan kuma yayin da muka ruɓanya wannan adadin da shinkafar noman daminan nan, za mu iya samun kusan tan miliyan 1.6 na shinkafa.

“Shi kuwa tan miliyan 1.6 na shinkafa, shi ne kusan kashi 27 na yawan shinkafar da ake buƙata a Najeriya, a kowace kakar noman shinkafa ko shekara.

“Idan har Jigawa za ta iya noma kashi 27 na yawan shinkafar da ake buƙata a ƙasar nan, to kenan haƙar mu ta cimma ruwa.

“Saboda haka za mu ci gaba da ƙarfafa manoma da goyon bayan shirin gwamnatin tarayya na ƙoƙarin bunƙasa ƙasa da wadataccen abinci,” inji Gwamna Namadi.

Yawancin gonakin noman shinkafar da Gwamna Namadi ya ziyarta, duk na ƙananan monoma ne, waɗanda suka taƙarƙare wajen ƙoƙarin himmar noma.

Sai dai kuma ba a san irin namijin ƙoƙarin da gwamnatin jiha da ta tarayya za su yi a wannan shekara wajen kauce wa ambaliya a lokacin damina ba.

People are also reading