Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Sanatan PDP da Ake Tuhuma da Buga Takardar NYSC Ta Bogi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wata babbar kotu da ke birnin tarayya Abuja ta sallami shari'ar da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da sanatan Bayelsa ta tsakiya, Benson Konbowei .
An gurfanar da Sanata Konbowei na jam'iyyar PDP tare da wasu mutane bisa zargin su da yin amfani da takardun kammala bautar ƙasa (NYSC) na bogi.
Mai shari'a Christopher Oba ya sallami Konbowei tare da soke tuhumar da ake yi masa jim kadan bayan lauyan da ke karar, Reuben Egwuaba ya nemi ayi hakan, in ji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barista Egwuaba ya shaidawa kotun cewa Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi, wanda ya sa aka shigar da karar, yanzu ya nemi a janye gaba daya.
Barista Egwuaba ya gabatar da bukata a gaban kotun na ta sallami sanatan da kuma rushe tuhumar, bukatar da lauyan wanda ake karar bai yi jayayya a kai ba.
Sai dai jaridar The Nation ta ruwaito cewa Mai shari'a Oba, wanda ya sallami Sanata Konbowei , bai karbi korafin lauyan wanda ake kara ba na a soke batun zargin gaba daya.
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tawagar jaridu 70 karkashin shirin fallasa rashawa (OCCRP) ta gano cewa Nasir El-Rufai ya mallaki gidan $193,084 a Dubai.
Abin mamaki, shekara daya kafin fitar da wannan rahoton, tsohon gwamnan na Kaduna ya yi rantsuwa da Allah cewa bai mallaki wani gida a wajen Najeriya ba.
Asali: Legit.ng