Home Back

'Yan Sanda Sun Yiwa Abba Kabir Martani Kan Umarnin Tuge Aminu Ado Daga Fadar Nassarawa

legit.ng 2024/7/3
  • Kwamishinan ƴan sanda a jihar Kano, Hussaini Gumel ya yi martani kan umarnin fitar da Aminu Ado daga fadar Nassarawa
  • Gumel ya ce ba za su bi umarnin Gwamna Abba Kabir ba tun da ya shigar da korafi a babbar kotun jihar kan lamarin
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya umarci kwamishinan ya fitar da Aminu Ado daga fadar Nassarawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta yi martani kan umarnin Gwamna Abba Kabir kan rushe fadar Nassarawa.

Kwamishinan ƴan sanda a jihar, Hussaini Gumel ya bayyana dalilin bijirewa umarnin gwamnan na fitar da Aminu Ado Bayero daga fadar.

'Yan sanda sun magantu kan umarnin Abba Kabir game da tuge Aminu Ado
'Yan Sanda sun ki bin umarnin tuge Aminu Ado da Abba Kabir ya yi a Kano. Hoto: Nigeria Police Force, Masarautar Kano. Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gumel ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar Punch ta wayar tarho a yau Juma'a 21 ga watan Yunin 2024.

Ya ce babu yadda za su bi umarnin gwamnan bayan ya shigar da korafi a babbar kotun jihar kan fitar da Aminu Ado daga fadar Nassarawa.

"Ƴan sanda ba za su bi umarnin gwamnan ba kan fitar da Amini Ado daga fada saboda gwamnatin ta shigar da korafi a babbar kotun jihar da za a yi hukunci a ranar Litinin 24 ga watan Yunin 2024."
"Bai kamata mu bi umarnin ba saboda sun shigar da korafi kan lamarin, idan muka dauki mataki kaman muna katsalandan ne ga kotun tun da ba mu san mene zai faru ba yayin hukuncin."

- Hussaini Gumel

Rahotanni sun tabbatar da an jibge jami'an tsaro a fadar musamman bayan umarnin gwamnan a jihar.

Yayin da kwamishinan ya ki bin umarnin gwamnan, Aminu Ado ya ci gaba da zama a fadar da fadawa da kuma dubban masoyansa.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading