Home Back

Amurka za ta kakaba wa Iran takunkumi saboda harin Isra'ila

dw.com 2024/5/17
Hoto: DW

Amurka na shirin kakaba wani sabon takunkumin karya tattalin arziki ga kasar Iran, a matsayin martani ga harin da ta kai wa Isra'ila a baya bayan nan.

Shugabar hukumar kula da baitulmalin Amurka Janet Yellen, ta ce suna tattaunawa da kawayensu don sanin irin takunkumin da ya dace sun sanya wa Iran da zai rage mata karsashi matuka.

Ta kara da cewa harin na Iran ga Isra'ila wani yunkuri ne na kara dagula zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya, tare da haddasa fantsamar tashin hankalin da yankin ke fama da shi.

People are also reading