Home Back

Iran Ta Kai Hari Kan Isra'ila, Ana Fargabar Barkewar Yaki a Gabas Ta Tsakiya

legit.ng 2024/5/20
  • Ƙasar Iran ta kai harin ramuwar gayya kan ƙasar Isra'ila inda ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa
  • Harin na zuwa ne bayan Isra'ila da kai hari kan ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus na ƙasar Syria
  • Hukumomi a Isra'ila sun ce sun kakkaɓo da yawa daga cikin makaman da taimakon sojojin Amurka da Birtaniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Iran ta harba ɗaruruwan makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a wani harin kai tsaye kan ƙasar Isra'ila.

Harin na Iran dai na ramuwar gayya ne bayan ta zargi Isra'ila da kai hari kan ofishin jakadancinta da ke birnin Damascus na ƙasar Syria.

Iran ta kai hari kan Isra'ila
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan Isra'ila Asali: Facebook

Jaridar Aljazeera ta ce harin na ramuwar gayyar ya raunata wata yarinya ƴar shekara bakwai da kuma haifar da ƴar ƙaramar ɓarna a wani sansanin sojin Isra'ila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin da aka kai a daren jiya Asabar ya sanya an kunna jiniyar tahowar makamai a biranen Isra'ila, ciki har da Tel Aviv da kuma yammacin Kudus.

An kuma ji ƙarar fashewar wasu abubuwa yayin da jami'an tsaron saman Isra'ila suka kakkaɓo makaman.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce makaman da Iran ta harbo sun ƙunshi sama da jiragen yaƙi marasa matuƙa 300 da makamai masu linzami, amma kaso 99% cikin 100% an kakkaɓo su, tare da taimakon sojojin Amurka da Birtaniya.

An harba makaman ne daga Iran, Iraq da Yemen.

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun tabbatar da kai harin, inda suka ce sun kai harin ne domin ramuwar gayya, rahoton BBC ya tabbatar.

An ƙaddamar da harin ne bisa atisayen 'True Promise' domin hukunta Isra'ila kan harin da ta kai a ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus, a ranar 1 ga watan Afirilun 2024.

Harin da aka kai a Damascus ya kashe mutum 12, ciki har da wasu manyan Janar-Janar guda biyu na dakarun Quds na IRGC.

Asali: Legit.ng

People are also reading